Gobara ta yi ajalin ’yar sakataren gwamnatin Sakkwato da ’ya’yanta 3

Tuni aka yi jana’izarsu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Gobara ta yi ajalin ’yar sakataren gwamnatin Sakkwato da ’ya’yanta 3

Gobara ta yi ajalin Rabi’atu Bello, ’yar Sakataren Gwamnatin Jihar Sakkwato, Bello Muhammad Sifawa, tare da ’ya’yanta uku da kuma ’yar aikinta.

Gobarar ta tashi ne a daren ranarLahadi a garin Sifawa da ke Ƙaramar Hukumar Bodinga a Jihar Sakkwato.

Wutar ta kama gidan, inda ita da ’ya’yanta uku; namiji guda ɗaya da mata biyu suka rasa rayukansu.

Sai dai mijinta, Muhammad Bello Yusuf, wanda shi ne babban sakatare a ma’aikatar matasa ta jihar, ya tsira tare da wasu ’ya’yansu biyu maza.

Rabi’atu, ita ce babbar ’yar Sakataren Gwamnatin Jihar Sakkwato.

An jana’izarsu a ranar Litinin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Yunƙurin jin ta bakin mahaifinta da mijin marigayiyar, ya ci tura saboda yanayi na alhini.