Gobara ta yi ajalin ’yar shekara 80 a Ogun
Gobarar ta tashi ne cikin dare yayin da mutanen gidan ke tsaka da barci.
Wata tsohuwa mai shekara 80, mai suna Mariam Salako, ta rasu sakamakon tashin wata gobara a Abeokuta, Babban Birnin Jihar Jihar Ogun.
Wutar ta tashi ne da sanyin safiyar ranar Asabar a wani gida da ke unguwar Ifelodun Agoka a Abeokuta.
- Zaɓe: Magoya bayan Ganduje sun shirya kawo tarnaƙi — Kwankwaso
- Cutar shan inna ta ragu da kashi 38 cikin shekara guda a Nijeriya — WHO
Kakakin ’yan sandan jihar, Omolola Odutola, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 1 na dare.
Amma ta ce har yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba.
Odutola, ta bayyana cewa an kira ’yan sanda don neman agaji, kuma Kwamandan yankin ya jagoranci tawaga zuwa wajen da lamarin ya faru.
Kazalika, Hukumar Kashe Gobara ta Jihar ta isa wajen kuma ta yi nasarar kashe wutar.
Sai dai, Mariam Salako da ke zaune a gidan ba a samu nasarar kuɓutar da ita ba, inda ta rasa ranta.
An ɗauke gawarta zuwa ɗakin ajiye gawarwaki.