Gobara ta yi barna a asibitin Tungar Magajiya

Gobara ta cinye dakin karbar marasa lafiya da dakin ajiye magunguna da dakin gwaje-gwaje da ofishin Sakataren babban asibitin Tungar-Magajiya da ke karamar Hukumar Rijau a Jihar Neja. Gobarar wadda ta tashi da misalin karfe 8:00 na safiyar Lahadin da ta gabata, ta janyo asarar miliyoyin Naira.Likitan asibitin Dokta Olukola ya shaida wa Aminiya cewa […]

Gobara ta yi barna a asibitin Tungar Magajiya
Gobara ta yi barna a asibitin Tungar Magajiya

Gobara ta cinye dakin karbar marasa lafiya da dakin ajiye magunguna da dakin gwaje-gwaje da ofishin Sakataren babban asibitin Tungar-Magajiya da ke karamar Hukumar Rijau a Jihar Neja.
Gobarar wadda ta tashi da misalin karfe 8:00 na safiyar Lahadin da ta gabata, ta janyo asarar miliyoyin Naira.
Likitan asibitin Dokta Olukola ya shaida wa Aminiya cewa gobarar ta samo asali ne sanadiyar maido da wutar lantarki daga kamfanin wutar lantarki na Najeriya kuma ya tabbatar da cewa dakunan da ake ajiye magunguna da wasu na gwaje-gwaje da inda ake ajiye katunan marasa lafiya da wasu muhimman wurare gobarar ta lalata su.
Sarkin Bauchin Rijau, Alhaji Muhammadu Bello Gidiya ya ce wa yanzu al’ummarsa za su kara shiga wani hali na la ha’ula’i, saboda wannan asibiti ne kadai talakan ya cin gajiya a garin, duk da cewa asibitin ya lalace.
Sarkin Bauchin Rijau ya kara da cewa, asibitin ya wuce shekara 70 da ginawa, inda yanzu ya zamo maboyar beraye da gafiyoyi, duk da cewa mutanen yankin sun sha kai kuka a gyara shi shekara da shekaru ba tare da an share musu hawaye ba.
Shugaban karamar Hukumar Rijau Alhaji Muhammad Bello Bako ya tabbatar da faruwar gobarar, inda ya ce, jama’ar gari ne suka kashe wutar saboda rashin hukumar kashe gobara a yankin.
Shugaban ya ce, an yi rubuce-rubuce da yawa a gwamnatin da ta shude amma duk tarihin wannan asibiti ba a kula da koken jama’ar ba, inda ya ce marasa gata ne ake kawowa asibitin, to yanzu ko marar gatan ba a san yadda za a yi da shi ba.
“A da wannan asibitin har makarantar horar da malaman jinya ake yi, saboda an gina shi tun kafin bayar da ’yancin kai, amma dubi abin bakin cikin da muke ciki,” inji shugaban.
Sai ya yi kira ga gwamnatin jihar ta dubi matsalolin da yankin ke ciki na karancin wurin kiwon lafiya da kayan aikin ceto da matsalar hanya domin kawo masa dauki.