Gobara ta yi barna a gidan Sheikh dahiru Bauchi

A ranar Talatar da ta gabata ce gobata ta tashi a tsohon gidan fitaccen malamin addinin Musuluncin nan Sheikh dahiru Usman Bauchi da ke Unguwar Makera kusa da Kasuwar Santaral da ke garin Bauchi.Gobarar ta cinye dukkan dakunan da ke saman benin gidan kafin jami’an Hukumar ’Yan Kwana-Kwana ta kawo dauki.Da yake zantawa da wakilinmu […]

Gobara ta yi barna a gidan Sheikh dahiru Bauchi
Gobara ta yi barna a gidan Sheikh dahiru Bauchi

A ranar Talatar da ta gabata ce gobata ta tashi a tsohon gidan fitaccen malamin addinin Musuluncin nan Sheikh dahiru Usman Bauchi da ke Unguwar Makera kusa da Kasuwar Santaral da ke garin Bauchi.
Gobarar ta cinye dukkan dakunan da ke saman benin gidan kafin jami’an Hukumar ’Yan Kwana-Kwana ta kawo dauki.
Da yake zantawa da wakilinmu a gidan daya daga cikin ’ya’yan Shehin Malami mai suna Malam Muhammad Fatihi, wanda wutar ta cinye dakunansa uku ya bayyana cewa haka kawai suka ga wuta ta tashi babu wanda zai iya cewa ga abin da ya haddasa gobarar.
“Amma muna godiya ga Allah babu wanda ya rasa ransa, sai dai kuma babu abin da aka dauka daga cikin dakunan. An shafe sama da sa’o’i uku zuwa hudu kafin a kashe wutar,” inji shi.
Ya ce mutane da dama sun kawo dauki amma saboda yadda iska ke kadawa sai wutar ta ci gaba da kamawa “Saboda haka muna mika godiya ga jama’a wadanda suka ba da gudunmawa don kashe gobarar. Da ma Shehi ya tashi daga gidan shekara takwas ke nan, yana gidansa da ke Unguwar kofar Wambai, amma babu abin da ya samu Masallacin Juma’ar da ke gidan a lokacin gobarar,” inji Malam Fatihi.
Ya ce lokacin da wutar ta tashi dukkan matan gidan ba sa nan, sai mace daya wadda ita ma dakinta ya kone da kayayyakinta da ke ciki. Ya ce daga cikin abubuwan da suka kone a lokacin gobarar baya ga kayayyakin daki akwai kayan abinci da littattafai da dimbin kayayyakin aiki na mata.
Sai ya mika godiyarsu ga Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Bauchi (SEMA), wadda Babban Sakataren Hukumar ya jatgoranci jami’anta suka ziyarci gidan domin gane wa idanunsu barnar da gobarar ta yi.