Gobara ta yi barna a kasuwar ’yan rake a Bauchi

Wata gobara da ta tashi a babbar kasuwar ’yan rake da ke bayan kasuwar shanu ta lakume shaguna da dama. Da yake zantawa da Aminiya a ofishinsa da ke kasuwar, shugaban kungiyar Alhaji Adamu Musa ya bayyana cewa an yi asarar sama da Naira miliyan 1.Ya ce a yanzu ’yan kasuwar suna cikin mawuyacin halin, […]

Gobara ta yi barna a kasuwar ’yan rake a Bauchi
Gobara ta yi barna a kasuwar ’yan rake a Bauchi

Wata gobara da ta tashi a babbar kasuwar ’yan rake da ke bayan kasuwar shanu ta lakume shaguna da dama.

Da yake zantawa da Aminiya a ofishinsa da ke kasuwar, shugaban kungiyar Alhaji Adamu Musa ya bayyana cewa an yi asarar sama da Naira miliyan 1.
Ya ce a yanzu ’yan kasuwar suna cikin mawuyacin halin, inda suke bukatar taimakon gaggawa.
Ya bukaci shugaban karamar Hukumar Bauchi, Alhaji Umar Aliyu ya taimaka musu da bohol a kasuwar, domin kowa ya san cewa sana’ar rake na bukatar tsaftataccen ruwa, inda ya bayyana kowace rana karamar hukumar tana samun kudin shiga a kasuwarsu sakamakon yadda ake sauke manyan motoci dauke da rake.