Gobara ta yi ta’adi a kasuwar Azare

Gobara ta tashi a babbar kasuwar Azare inda ta lashe kayayyaki na miliyoyin naira ranar alhamis da dare, lamarin da ‘yan kasuwa da mazauna garin na Azare suka ce ba su taba ganin barnar wuta a kasuwar kamar na wannan lokaci ba.Wutar, wacce ta tashi da misalin karfe biyu na dare, ta lashe rukunin wadansu […]

Gobara ta yi ta’adi a kasuwar Azare
Gobara ta yi ta’adi a kasuwar Azare

Gobara ta tashi a babbar kasuwar Azare inda ta lashe kayayyaki na miliyoyin naira ranar alhamis da dare, lamarin da ‘yan kasuwa da mazauna garin na Azare suka ce ba su taba ganin barnar wuta a kasuwar kamar na wannan lokaci ba.
Wutar, wacce ta tashi da misalin karfe biyu na dare, ta lashe rukunin wadansu shaguna, inda ta janyo asarar dukiya ta miliyoyin naira, kuma an dauki tsawon lokaci ana aikin kashe gobarar don ganin an kange ta daga fadawa wadansu wurare da ake ganin za ta kara lalatawa.
Shugaban kwamitin riko na karamar hukumar Katagum Alhaji Abubakar Dahuwa Abdulkadir da kansiloli da shugabannin sassa sun kai ziyarar jaje ga ‘yan kasuwar, shi ma Wazirin Katagum Alhaji Sule Katagum ya yi wa wadanda wutar ta lashe musu dukiya mai tarin yawa jaje, inda ya jajanta musu tare kuma da alkawarin rubuta wa gwamnatin Jihar Bauchi da hukumomin da suke taimakawa don ganin an agazawa ‘yan kasuwar da suka yi wannan asara don su samu inda za su farfado da arzikinsu. Ya kuma ya jawo hankalin ‘yan kasuwa a kan su rika kashe wutar shagunansu da dare, saboda ana zaton wutar mai yiwuwa ta tashi ne a sakamakon matsalar wutar lantarki.
Shi ma makaman Katagum da Hakimai sun kai irin wannan ziyarar a madadin masarautar Katagum,  inda suka jajantawa ‘yan kasuwar game da wannan asara da ta same su, inda suka yi fatan Allah Ya mayar musu da alheri game da wannan jarrabawa da ta same su.