Gobarar barayin danyen mai ta kashe mutane da dama

Mutane da yawa sun mutu a gobararda da ta tashi a sakamakon rikicin da ya barke tsakanin barayin danyen mai a Jihar Imo.

Gobarar barayin danyen mai ta kashe mutane da dama

Mutane da yawa sun mutu a gobararda da ta tashi a sakamakon rikicin da ya barke tsakanin barayin danyen mai a Jihar Imo.

Fashewar haramtacciyar matatar man ta kuma kone gidaje da gonakin a  yankin na Obitti da ke Karamar Hukumar Ohaji/Egbema ta jihar.

Gobarar ta tashi ne a lokacin da masu satar danyen mai suke kwasar man da suke kokarin loda man satan da suka adana a karkashin kasa zuwa a cikin wata jirgin ruwan dakon mai.

Aminiya ta gano cewa barayin man sun yi haka wani rami mai zurfi, inda suke boyen man nasu, wanda suke diba ta wani bututu da suka dasa suke satar mai daga babba bututun man gwamnati.

Wani ganau ya ce suna cikin koda man nasu ne gungun wasu ’yan daba suka kai musu hari, inda bangarorin suka yi musayar wuta da ta haddasa gobarar da ta kashe mutane da dama ta kona kadarori, ciki har da jirgin ruwan.

Wakilinmu ya ce mazauna yankin suna yin kaura don guje wa tambayoyin jami’an tsaro.

Kakakin ’yan sandan jihar Imo, ASP Henry Okoye ya ce rundunar ta kafa kwamitin binciken lamarin da kamo masu hannu a ciki bisa umarnin Kwamishinn ’yan sandan jihar, CP Aboki Danjuma.

Sai dai ya ce ba zai iya tabbatar da yawan mutanen da suka mutu ba.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos