‘Gobarar cibiyar kayayyakin gargajiya ta jawo mana koma bayan kasuwanci’

Masu kasuwancin kayayyakin gargajiya a Abuja na fuskantar karancin abokan hulda musamman baki daga kasashen waje wadanda a baya ke zuwa kasuwarsu domin harkokin kasuwanci. Yanzu masu kayayyakin suna gudanar da harkokinsu ne a mabambanta wurare maimakon a cibiyarsu da ke daura da otel din Sharaton da ke Abuja, wadda gobara ta shafa kusan shekara […]

‘Gobarar cibiyar kayayyakin gargajiya ta jawo mana koma bayan kasuwanci’

Masu kasuwancin kayayyakin gargajiya a Abuja na fuskantar karancin abokan hulda musamman baki daga kasashen waje wadanda a baya ke zuwa kasuwarsu domin harkokin kasuwanci.

Yanzu masu kayayyakin suna gudanar da harkokinsu ne a mabambanta wurare maimakon a cibiyarsu da ke daura da otel din Sharaton da ke Abuja, wadda gobara ta shafa kusan shekara daya da ta gabata.

Aminiya ta ziyarci daya daga cikin wuraren da suka koma da ke kusa da shatale-talen Life Camp a Abuja, inda ’yan kasuwar suka yi korafin cewa harkoki sun yi sanyi a yanzu kasancewar yawancin baki musamman na waje da suka samu kansu a Abuja, na kaurace wa wajen saboda dalilan tsaro.

Wani da wakilinmu ya zanta da shi mai suna Zakariyya Garba ya ce ya koyi harkar ce daga wajen iyayensa tun suna Legas. Ya ce mahaifinsa ya dawo Abuja ce a lokacin da aka bude cibiyar da ta kone a shekarar 2003 inda tsohon Ministan Abuja Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i ya raba musu shagunan bukkoki don tallata kayan gargajyar Najeriya ga baki da suka zo bikin taron Kasashen Rainon Ingila da aka (CHOGM) da kasar nan ta karbi bakuncinsa.

Malam Zakariyya Garba ya ce wajen ya ci gaba da samun bunkasa har zuwa lokacin da gobara  ta auku, inda Hukumar   Al’adun Gargajiya ta Kasa (NCAC) ta rufe cibiyar.

Malam Zakariyya wanda dan asalin Jihar Kano ne, ya ce mambobinsu da suka rasa matsuguni tun lokacin suna da yawa. “Ni din nan da ka samu a rumfar nan mun kai mu hudu kuma abokinmu ne ya ba mu damar zama a wajen kasancewar sun jima a wannan waje tun gabanin rufe inda muka baro,” inji shi.

Malam Auwal Sulaiman wanda dan asalin Jihar Kastina ne, na cikin wadanda ke da shago a kasuwar ta baya. Sai dai ya ce a yanzu haka ya gwammace dauko kaya daga jiharsu ya sarar ga masu rumfuna ko ya yi talla, kasancewar har yanzu bai samu matsuguni ba. Ya ce mambobinsu da dama sun kafa rumfuna a kusa da lambun shakatawa na Millanium Park da ke Abuja bayan rufe cibiyar tasu, sai dai a cewarsa hukuma ta rusa rumfunan bayan sun kashe makudan kudi ciki har da biyan wani da ya danganta kansa da wajen.

Aminiya ta ziyarci cibiyar da aka rufe, inda ta gano cewa ba wata alamar aikin gyara wajen in ban da jami’an tsaro na wani kamfani da suka aje zango a kusa da babbar kofar shiga cibiyar. Yunkurin da wakilinmu ya yi na karasawa kusa da kofar cibiyar ya fuskanci turjiya daga wajen masu tsaron inda suka umarce shi da ya koma baya, bayan ya fara daukar hoto.

Lokacin da aka tuntubi shugaban kungiyar masu sana’a da kuma sayar da kayan gargajiya ta cibiyar Mista Nze Kanayo ya bayyana  rufe wajen da wata shiryayyiya da Hukumar NCAC a karkashin jagorancin Babban Daraktanta Otunba Segun Runsawe ta yi don raba su da wajen da kuma mika wajen ga masu zuba jari kamar yadda ya yi zargi. Ya ce kimanin mambobinsu 92 ne wadanda suka dauki matakin kwana a cibiyar don tsare dukiyarsu bayan gobarar wadda ya ce ke dauke da alamar tambaya, aka kama a cewarsa tare da gurfanar da su a gaban kotu a matsayin masu laifi.

Malam Mahmud Mahmud na daga cikin wadanda rufe wajen ya shafa kasancewar kamfaninsa mai suna Ummakhalif ya gina shago 21 a cibiyar kan tsarin gwamnati na zuba hannun jari don cin gajiyar shagunan na tsawon shekara 25, kafin sake sabunta ’yarjejeniyar ko kuma soke ta, kamar yadda ya bayyana.

Sai dai ya ce yarjejeniyar wadda kamfaninsa ya cimma da Ma’aikatar Kula da Birnin Tarayya ya fuskanci sabawar ka’ida gabanin cikar wa’adin a lokacin da ma’aikatar kula da Birnin Tarayya karkashin tsohon Minista Bala Muhammad ta mika ragamar mallakar cibiyar  ga Ma’aikatar Watsa Labarai da Al’adun gargajiya ta Tarayya, wadda Hukumar NCAC ke karkashinta. Ya ce sun wayi gari da samun labarin ne a jarida ba tare da an tuntube su ba.

Gaba dayan bangarorin biyu wato kungiyar ma’abota cibiyar da kuma kamfanin na Ummakhalif, sun shigar da kara a gaban kotu, kan matakin da Hukumar NCAC ta dauka inda a yanzu haka ake ci gaba da sauraron lamarin.