Gobarar kasuwar Bwari: A yi koyi da Ali Dogo – Sarkin Bwari

Mai martaba Sarkin Bwari da ke birnin Tarayya, Abuja, Alhaji Auwal Musa Ijakoro II ya nemi attajirai da daukacin al’umma su yi koyi da Alhaji Aliyu Salihu, wanda aka fi sani da “Ali Dogo” wajen kai dauki ga ’yan kasuwa, musamman masu karamin karfi da suka rasa dukiyarsu sakamakon gobarar da ta shafe su a […]

Gobarar kasuwar Bwari: A yi koyi da Ali Dogo – Sarkin Bwari

Mai martaba Sarkin Bwari da ke birnin Tarayya, Abuja, Alhaji Auwal Musa Ijakoro II ya nemi attajirai da daukacin al’umma su yi koyi da Alhaji Aliyu Salihu, wanda aka fi sani da “Ali Dogo” wajen kai dauki ga ’yan kasuwa, musamman masu karamin karfi da suka rasa dukiyarsu sakamakon gobarar da ta shafe su a babbar kasuwar Bwari mako biyu da suka gabata.

Sarkin ya yi wannan kira ne a ranar Juma’ar da ta gabata,  lokacin da yake amsar tallafin shinkafa buhu 50 da Ali Dogo, Kansila mai wakiltar Kubwa, a karamar Hukumar Bwari ya ba da domin rabawa ga mutanen da gobarar ta shafa. Ya nemi al’umma su zauna lafiya da juna, su kiyayi ta da fitina, wadda a cewarsa idan ta taso, za ta shafi mai laifi da ma wanda bai ji ba bai gani ba.

“Wadanda gobarar nan ta shafa suna cikin matsi, musamman wadansu ma ba su da abin da za su ci su da iyalinsu, domin sun rasa komai nasu a kasuwar da ta kone. Akwai wata mata da mijinta ya mutu ya bar ta da ’ya’ya. Da kudin fanshon mijin nata ta samu rumfa a kasuwar, inda ta haka take daukar dawainiyar abinci da sutura da karatun yaran, amma yanzu komai ya kone, ba su da abin da za su ci. Don haka lallai ne masu hali su kawo dauki, domin saukaka masu wannan matsala,” inji Sarkin na Bwari.

A bangaren Kansila Ali Dogo ya shaida wa wakilinmu cewa ya yi  alhini a lokacin da ya ga irin matsalar da al’ummar Bwari suka shiga sakamakon  gobarar. 

“A matsayina na shugaban al’umma, ya zama dole in yi amfani da damar da Allah Ya ba ni, domin tallafa wa al’ummata. Wannan shinkafa buhu 50 da na ba da, na bayar ne domin jinkai da tausayi. Kuma ina kira ga sauran al’umma, musamman masu hannu da shuni su taimaka,” inji shi.