Gobarar kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi: `Yan kasuwa na matukar bukatar tallafin gaggawa

Mai yiwuwa mai karatu a lokacin da kake karanta wannan makala, an kammala aikin kwashe buraguzan gobarar kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi da aka fi sa ni da kasuwar Sabon garin Kano, da aka yi fama da ita tun a cikin daren Asabar da ta gabata, ta kai kuma har ranar Talatar nan ana samun burbushinta […]

Gobarar kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi: `Yan kasuwa na matukar bukatar tallafin gaggawa
Gobarar kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi: `Yan kasuwa na matukar bukatar tallafin gaggawa

Mai yiwuwa mai karatu a lokacin da kake karanta wannan makala, an kammala aikin kwashe buraguzan gobarar kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi da aka fi sa ni da kasuwar Sabon garin Kano, da aka yi fama da ita tun a cikin daren Asabar da ta gabata, ta kai kuma har ranar Talatar nan ana samun burbushinta nan da can. Haka kuma ana sa ran zuwa yanzu din Kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa a karkashin shugabancin Alhaji Ali dan Bagadaza, da aniyar ya iya bata shawara akan kiyasin barnar da aka yii da irin taimakon da za a yi wa `yan kasuwar da inda za a tsugunnar da su shi ma ya kammala aikinsa.
An ruwaito Darakta Janar na Hukumar bayar da agajin gaggawa na kasa baki daya, Alhaji Sani Sidi, a yayin ziyarar jaje da gani da ido da aniyar kididdige asarar da aka yi da ya kai kasuwar a ranar Lahadin da ta gabata, yana fadin cewa, gabarar ta kasuwar Sabon gari, ita ce gobara ma fi girma da muni da aka taba yi a tarihin gobarar kasuwanni a kasar nan baki daya. Gobarar da zuwa yanzu ana kyautata zaton ta haddasa asarar kayayyaki da kaddarori, kai har ma da tsabar kudi da ake kiyasin sun kai na Naira tiriliyan biyu ( =N=2tiriliyan), inda ta shafi rumfuna da shaguna da kantuna 3,800, adadin da ake kiyasin shi ne kusan kashi uku cikin hudu na yawan rumfunan kasuwar gaba dayanta. Darakta Janar din, bayan jajanta wa `yan kasuwar da ya yi ya kuma ba su tabbacin cewa, da zarar jami`an Hukumarsa sun kammala tantance barnar da gobarar ta yi, hukumarsa za ta kawo agajin gaggawa gare su.
Shi ma mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II, wanda yana wani bulaguro a kasashen waje ya samu labarin tashin gobarar, inda nan da nan ya yanke ziyarar ya dawo gida,bayan ya kammala jajanta wa `yan kasuwar, sai kuma ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha da lallai su binciki musabbabin tashe-tashen gobara a kasuwanni da wasu makarantun jihar ta Kano da ake ta fama da su a `yan kwanakin nan, sannan kuma ya nemi gwamnatin jihar da ta hanzarta sake tsare-tsaren kasuwannin jihar, ta yadda za su dace da zamani. Sarkin, ya kuma shawarci `yan kasuwa da su rumgumi akidar yin inshoran Musulunci ta Takaful, ta yadda za su rinka rage asarar da ta ka same su a annoba irin wannan.
Gobarar ta kasauwar Sabon gari ta wannan karo ta zo ne sama da wata guda bayan makamanciyar irinta, wato ta kwanar kasuwar Singa da suke hannun riga da kasuwar ta Sabon gari,wadda aka yi asarar kayayyaki da kaddarori na sama da Naira biliyan biyu (=N=2biliyan). Da sake samun tashin wannan gobara ta kasuwar Sabon garin, yanzu gwamnatin Jihar Kanon ta kara wa`adin makonni biyu ga Kwamitin mai shari`a Wada Rano, da yake binciken musabbabin tashin waccan gobara ta Kwanar Singa, don ya binciki wannan ta kasuwar Sabon garin. Kasuwar dai ta Sabon gari mallakin kananan hukumomin jihar shidda ce da huruminsu yake cikin kwaryar birnin Kano da kewaye, ya yin da sauran Kasuwanni suke mallakin majalisun kananan hukumomin da suke ciki. Dama dai a lokacin hunturu aka fi samun tashe-tashen gobara a kasar nan, don koda a ranar Asabar da ta gabata sai da aka samu makamanciyar tashin irin wannan gobara a babbar Kasuwar Birnin Kebbi, Hedkwatar Jihar Kebbi da zuwa yanzu aka yi kiyasin ta kone rumfuna 2,494, da dukiya da kaddarori na miliyoyin Naira.  Bayan wadannan gobara biyu a Kano, an kuma samu tashin gobara a kasuwar `yan Katako ta da `yan Lemo dukkansu a Na`ibawa da ta `yan waya da ke gidan gona da ta Kurmi da ta `yan kujeru a unguwar Gandun Albasa, baya ga a Makarantun Sakandaren gwamnatin jihar kusan takwas a banan.
Kamar yadda har yanzu ba a iya tantance musabbabin tashe-tashen wadancan gobara da na ambata ba, sai dai shaci-fadi da ake ta yi, haka ita ma ta Kasuwar Sabon garin, da wasu suka ce daga na`urar taransifomar kasuwar ta tashi bayan an kawo wutar lantarki a tsakar dare, yayin da Kamfanin bayar da wutar lantarki na shiyyar, wato KEDCO, ya musanta cewa, yau sama da shekaru biyu, ta tsinke hanyar bayar da wutar lantarki a kasuwar,don haka, tunda ba su ba da wuta a kasuwar me ya kawo a ce na`urar tiransifomarsu ce ta yi bindiga bayan an kawo wuta?
Yawan tashin gobara a kasuwar ta Sabon gari ya sanya bayan tashin wata gobara a kasuwar a wajen shekarar 1984, lokacin gwamnatin mulkin soja ta Eya Kwamando Hamza Abdullahi ta gina kasuwar ta Sabon gari a zaman ta zamani, ta kuma rage cunkosonta, ta hanyar samar da kasuwar `yan hatsi a Dawanau da ta masu Lemo da Katako a unguwar Na`ibawa da ta kayan gwari a unguwar `yan Kaba. Amma yanzu maganar da ake ciki, dukkan kasuwannanin da ke birnin Kano da kewaye, musamman kasuwannanin Sabon gari da Kwanar Singa da ta Kantin Kwari da ta kofar Wambai da Kasuwar Kurmi, duk a cike suke, ta yadda ba wai abin hawa ba, mutum da mutum ma wahalar shiga kasuwannin suke samu, saboda tsananin cunkoson da suke ciki,ta yadda kowane layi da bakin kanti ko rumfa za ka tarar an kafa tebur, wanda son a samu kudi kawai ya kawo shi bisa hadin bakin masu kantuna da shaguna da rumfuna da shugabannin kungiyoyin `yan kasuwar.
Wannan cunkoson kasuwanni yana taimakawa kwarai da gaske cikin ta`azzarar yaduwar gobara a duk lokacin da ta tashi kamar yadda aka gani a gobarar kasuwar Sabon gari a makon jiya da wadda aka yi fama da ita a wani bangare na kasuwar kwanar Singa, ta yadda `yan kwana-kwana suka rinka fuskantar matsalar kashe gobarar a kan rashin hanyoyin da motocinsu za su shiga. Rashin lafiyayyu kuma ingantattun motoci da na`urori da sinadaran kashe gobara da Kano ta dade tana fama da su, su ma suna taimakawa gaya a koda yaushe wajen aikin kashe gobarar cikin gaggawa. Ko a wannan karon sai da aka ji gwamnan jihar a lokacin ziyarar jaje da ya kai wa `yan kasuwar yana ba su tabbacin cewa, gwamnati za ta wadata hukumar kashe gobarar da motoci da na`urorin da take bukata.
Idan mai karatu ya yi nazarin yawan tashin gobarar da ake yawan samu a kasuwannin kasar nan zai ga cewa akwai sakaci da rashin kulawar `yan kasuwar, wajen rashin kulawa da abin da zai cuce su da daukar matakan da suka kamata don magance su. Don haka `yan kasuwa ya kamata su rinka tanadar wa da kansu abubuwan da suka hada da maotoci da na`urorin kashe gobara, gwamnati ta ba su ma`aikata. kungiyoyin `yan kasuwar ya kamata su rinka yakar wanda duk ya nemi ya kawo musu cinkoso ta kowace hanya a kasuwanninsu, koda kuwa shugabannin majalisun  kananan hukumomi ne. Ya kuma kamata su rinka yin inshoran Takaful akan dukiyoyinsu kamar yadda mai Martaba Sarkin Kano ya ba su shawara.
Daga bangaren gwamnatoci ya kamata su tabbatar da ana bin doka da oda da hukunta dukkan wanda aka samu yana karya tsarin tafiyar da kasuwannin. Akwai bukatar daga bana gwamnatin jihar Kano ta yafe wa dukkan `yan kasuwar da rumfunansu ko gine-ginensu suka kone a dukkan kasuwannin da aka samu ibtala`in gobarar biyan kudin haya da na haraji har na tsawon shekaru uku zuwa biyar. Kazalika akwai bukatar Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da wani asusu da za ta nemi gwamnatin tarayya da na jihohi da majalisun kananan hukumomin kasar nan da Kamfanoni da kungiyoyin ba da tallafi na kasa da kasa da masu masana`antu da duk masu hannu da shuni na ciki da wajen kasar nan da za su bayar da gudummuwa don sake tsugunnar da dukkan wadanda suka hadu da wannan ibtila`in.