Gobarar kyandir ta kashe yarinya mai shekara 8

Wutar ta tashi a yayin da yarinyar take barci a cikin daki.

Gobarar kyandir ta kashe yarinya mai shekara 8

Gobara

Wata yarinya mai shekara takwas a duniya ta rasa ranta sakamakon tashin wata gobara a yankin Ugwuaji da ke Karamar Hukumar Enugu ta Kudu a Jihar Enugu.

Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta Jihar, Cif Okwudili Ohaa, ya tabbatar wa Kamfanin Dillacin Labarai (NAN) da faruwar lamarin, inda ya ce gobarar ta lakume kadarori na miliyoyin kudi.

Ohaa ya ce jami’an kashe gobarar jihar sun kai dauki bayan samun kiran agaji da misalin karfe 8:30 na daren Alhamis a unguwar Umunnaugwu.

Ya ce sun yi kokari wajen ceto duk mutanen da ke cikin wasu dakuna 10 a gidan mai dakuna 14.

“Jami’anmu sun yi nasarar ceto mutane da dama daga wutar, amma kafin zuwanmu an yi rashin sa’a wutar ta cinye wani daki da wata karamar yarinya take barci a ciki.

“Mun jajanta wa iyayen yarinyar, muna fatan Ubangiji Ya ba su hakuri da juriyar rashinta,” a cewarsa.

Da yake tattaunawa da manema labarai, kakan yarinyar da ta rasu, Mista Lazarus Anya-Anike, ya ce wutar ta tashi ne sakamakon tashin wutar kyandir, wanda yara suke amfani da shi wajen karatun dare.

“Jikata Ifunanya mai shekara takwas tana ciki lokacin da wutar ta tashi, su kuwa sauran yaran sun fice.

“Amma jami’an kashe gobara sun kashe wutar daga bisani.

“Sun yi kokarin kashe wutar a kan lokaci wanda hakan ya hana wutar ta cinye ginin baki daya,” inji Anya-Anike.

Ya roki gwamnatin jihar da sauran al’umma da su tallafa wa iyalansa sakamakon yadda wutar ta salwantar musu da dukiya.