Gobarar motar tanka ta kone gidaje da motoci a Legas
Akalla gidaje 4 ne suka kone a lokacin da wata babbar motar tanka dauke da man fetur ta fado daga saman gadar Oju-elebga a Legas, inda man fetur din da ta dauko ya kwaranye, ya malala ko’ina; ya bi ta magudanan ruwa kana daga bisani ya kama da wuta; a inda ya kone motoci biyar […]
Akalla gidaje 4 ne suka kone a lokacin da wata babbar motar tanka dauke da man fetur ta fado daga saman gadar Oju-elebga a Legas, inda man fetur din da ta dauko ya kwaranye, ya malala ko’ina; ya bi ta magudanan ruwa kana daga bisani ya kama da wuta; a inda ya kone motoci biyar da gidaje hudu da ke daura da wajen, koda yake ba a sami asarar rai ba.
A sakamon gobarar, mutanen yankin sun yi ta gudun tsira da rai. Motar tankar mallakar kamfanin Forte Oil, ta fadi ne a daidai wurin da motar mai dauke da kwantaina ta fadi ta kashe mutane uku a ’yan watannin da suka shige.
A cewar shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Legas, Micheal Akindele, hatsarin ya faru ne da misalin karfe 2:15 na dare kana gobarar ta kone gidaje hudu, inda daya daga ciki ne ya kone kurmus, yayin da saukan ukun sassansu suka kone. Gobarar ta kuma kone motoci guda biyar, inda ya ce motar ta fado ne a lokacin da take kokarin hawa gadar.
A nasa bangaren, babban daraktan hukumar kashe gobara a Jihar Legas, Rasak Fadipe ya shaida cewa motar na dauke da manfetur lita 33,000 a lokacin da ta fadi ta kama da wuta kuma jami’an kashe gobara sun yi iya kokarinsu wajen hana wutar kai wa ga sassan unguwannin yankin.