Gobarar tankar gas ta kashe mutum 2, ta jikkata 200 a Kenya
Akalla mutum sama da 200 ne suka jikkata a yankin.
Akalla mutum biyu ne suka rasu, yayin da wasu fiye da 200 suka jikkata lokacin da wata mota dauke gas ta yi bindiga a Nairobi, Babban Birnin Kasar Kenya.
Gobarar ta tashi ne a daren Alhamis a unguwar Embakasi a Kudu Maso Gabashin babban birnin kasar.
- ’Yan fashi 8 sun shiga hannu a Kaduna
- Cire tallafin man fetur alheri ne ga Najeriya — Ministan Labarai
“Wutar ta kone abubuwa da dama, ta lalata gidaje masu yawa,” in ji hukumomin kasar.
“Gobarar ta kara lalata motoci da dama da dukiyoyin ‘yan kasuwa.
“Gidajen jama’a da ke yankin da abun ya faru sun kama da wuta.”
Bayan rasuwar mutum biyu, an garzaya da sama da mutum 222 asibitoci daban-daban don kula da su.
Kungiyar Agaji ta Red Cross ta Kenya, ta ruwaito cewar akalla mutum kusan 300 ne suka jikkata.
Hukumomi a yankin sun bayyana cewar mazauna yankin na kwana a waje ne sakamakon yadda gobarar ta lalata musu muhallai.
Wasu da dama a yankin sun fara kwashe kayansu suna neman matsuguni a wasu yankunan kasar.