Gobarar Tankar Mai A Legas: kalubale Ga Gwamna Ambode

Bala’in gobara da ke aukuwa a kai-a kai a sassan Jihar Legas, da ke jaza asarar rayuka da dukiyoyi masu yawan gaske ya zama babban kalubale ga sabuwar gwamnatin jihar. Tun bayan da aka rantsar da sabon Gwamnan jihar, Akinwunmi Ambode aka rika samun aukuwar gobara a wurare daban-daban a jihar wadanda suka hada da […]

Gobarar Tankar Mai A Legas: kalubale Ga Gwamna Ambode
Gobarar Tankar Mai A Legas: kalubale Ga Gwamna Ambode

Bala’in gobara da ke aukuwa a kai-a kai a sassan Jihar Legas, da ke jaza asarar rayuka da dukiyoyi masu yawan gaske ya zama babban kalubale ga sabuwar gwamnatin jihar.

Tun bayan da aka rantsar da sabon Gwamnan jihar, Akinwunmi Ambode aka rika samun aukuwar gobara a wurare daban-daban a jihar wadanda suka hada da kasuwanni da kuma unguwannin jihar.
Kwanaki kadan kafin a rantsar da gwamnan, Gwamnatin Fashola da ta shude ta sha fama da bala’in gobara ta rika auka wa jihar inda kasuwanni da yawa suka kone wadanda suka hada da kasuwar katako ta Makoko da kasuwar cikin birnin Ikko da sauransu, inda aka yi asarar shaguna da rayuka da kuma hajoji na miliyoyin kudi.
To amma sai kwanakin kadan da rantsar da sabuwar gwamnatin jihar bala’in gobarar ya dauki sabon salo inda tankokin mai suka rika haddasa shi sakamakon zargin tukin ganganci na direbobin tanka.
Bala’in gobarar da ya auku a kan mahadar titin Yanafaja shi ya fi daukar hankulan jama’a inda shaguna 40 suka kone yayin da tankar ta fado daga kan gadar Yanafaja ta kama da wuta, inda gidaje 20 suka kone motocin jama’a guda 20 suka kone.
Sai gobarar da ta auku a yankin Idimu inda shaguna 70 suka kone gidaje da dama suka kone bayan da wata tanka dauke da man fetur ta kama da wuta a yankin.
Bala’in gobarar ya tayar da hankalin sabon gwamnan jihar, Ambode inda ya dora alhakin aukuwar lamarin a kan rashin da’a da tukin ganganci na direbobin tankar mai.
Gwamnan ya yi alwashin daukar matakan da suka dace wajen kawo karshen hadarin tankar mai a jihar. Ya gayyaci kungiyar direbobin tanka da masu ruwa da tsaki a jihar babban taro don gano bakin zaren matsalar a jihar.
To amma jama’a sun sanya ido su ga sababbain matakan da sabuwar gwamnati za ta dauka don maganin matsalar a jihar.