Gobarar tankar mai ta yi ajalin mutum 18 a Enugu

Hatsarin wanda ya auku sakamakon shanyewar birki ya rutsa da ababen hawa 17.

Gobarar tankar mai ta yi ajalin mutum 18 a Enugu

Wata tankar mai da ta kama da wuta

An tabbatar da mutuwar aƙalla mutum 18 sakamakon hatsarin wata tankar mai da ta yi bindiga a Jihar Enugu.

Alƙaluman da mahukunta suka fitar ya nuna cewa hatsarin ya rutsa da mutum 31 ciki har da mutum 10 da suka samu raunuka daban-daban yayin da aka ceto wasu uku da suka tsallake rijiya da baya sai kuma mutum 18 ɗin da suka ƙone ƙurmus.

Hakan na ƙunshe cikin sanarwa da mai magana da yawun rundunar hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa reshen Jihar Enugu, Olusegun Ogungbemide ya fitar da yammacin ranar Asabar.

Sanarwar ta bayyana cewa hatsarin wanda ya auku a sanadiyyar shanyewar birki ya shafi ababen hawa 17 da suka haɗa da tanka ɗaya, motoci 15 da kuma wani babu mai ƙafa uku.

Bayanai sun ce an shiga ruɗanin lokacin da tankar fetur ɗin ta yi bindiga, yayin da take saukowa daga wata hanya mai gangara a wani babban titi mai cunkoso a jihar ta Enugu.

TRT ta ruwaito cewa Kwamandan Hukumar Kare Haɗura ta Ƙasa a jihar, Franklin Agbakoba Onyekwere ya ce ya je wajen amma bai yi ƙarin bayani ba.

Tankar man ta kama da wuta ne ƙasa da mako guda bayan mutane fiye da 100 sun mutu yayin da wata tankar mai ta yi bindiga a Jihar Neja.

Kamfani Dillancin Labarai na Anadolu ya ba da rahoton cewa, Nijeriya ta fuskanci hatsarin tankar mai 172 inda mutane 1,896 suka mutu tun daga 2009, a yayin da matsalar ta fi muni a 2024, inda jimillar mutanen da suka mutu suka kai 266.