Gobarar tankar fetur ta kashe direbanta a Ibadan
Faɗuwar tankar man ke da wuya ta kama da wuta, inda daga bisani ta yi bindiga ta ƙone direbanta ƙurmus har lahira a cikinta.
Wata tankar man fetur ta yi bindiga bayan da ta yi taho-mu-gama da wasu manyan motoci biyi a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.
Faɗuwar tankar man ke da wuya ta kama da wuta, inda daga bisani ta yi bindiga ta ƙone direbanta ƙurmus har lahira a cikinta.
Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2.30 na dare, bayan tankar ta ƙwace a hannun direbanta ta yi karo da wasu manyan motoci biyu sannan ya yi adungure, a yankin Fijabi da ke Babbar Hanyar Ojoo zuwa Iwo a ranar Laraba.
Darakta Janar na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Oyo, Yemi Akinyinka, bayyana cewa “direban tankar man fetur ɗin ya rasu, yaron motar guda ɗaya kuma ya samu rauni ana kula da shi a Asibitin Koyarwar na Jami’ar Ibadan.”
Akinyinka ya tabbatar cewa ,an fetur ne motar ta ɗauko amma ya bayyana cewa gaggawar kawo ɗauki da ka yi ta taimaka wajen hana sauran manyan motocin su kama da wuta.