Gobarar tanki ta halaka mutum 8 a Tafa
Wata gobarar fetur da ta biyo bayan hadarin tankar mai a garin Tafa da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna ta halaka mutum 8 da kuma raunata karin mutum 15, yayin da wani otel ya kone kurmus, a ranar Asabar da ta gabata. Lamarin wanda ya faru da misalin karfe takwas na safe, ya kuma […]

Wata gobarar fetur da ta biyo bayan hadarin tankar mai a garin Tafa da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna ta halaka mutum 8 da kuma raunata karin mutum 15, yayin da wani otel ya kone kurmus, a ranar Asabar da ta gabata.
Lamarin wanda ya faru da misalin karfe takwas na safe, ya kuma kona shaguna 12 da aka gina a jikin wani gidan karuwai tare da dakunan matan, da kuma tarin bacoci da ke kan titi da suka hada da na sayar da abinci da sauran wuraren sana’o’i kamar kanikancin manyan motoci da ruwaya da masu gashin nama sai kuma masu sayar da kayan gyaran motocin da kuma ’yan bunburutu.
Wakilinmu da ya sake komawa garin a yammacin ranar Talatar da ta gabata, ya samu labarin cewa adadin ya karu ne daga jimla na farko bayan wasu da aka garzaya da su asibiti a sakamakon raunukan kunar, sun rasu daga bisani. Aminiya ta samu labarin cewa hatsarin dai ya biyo bayan tahowar wata tankar mai da ke dauke da sunan “Shema Petroleum Ltd” daga bangaren Kaduna da ta ishe layin motoci a kan titin, inda direbanta ya yi kokarin tsayawa amma ba tare da nasara ba.
Bayanan sun ce a kokarinsa na kauce wa jerin gwanon motocin, dereban tankar ya takura motarsa ta jikin dakalin Babangida, inda kan motar ya samu wucewa amma sai kumburin tankin ya karci jikin wata tankar mai da ke kan jerin gwanon, al’amarin da ya haddasa tsagewar bangaren tankin motar, sannan mai ya rika kwarara zuwa cikin magudanan ruwa.
A cewar wasu da Aminiya ta zanta da su: “Wasu matasa sun bazama cikn magudanan ruwan dauke da jarkoki da kuma bokiti, inda suka rika kwasar mai suna kai wa ta bangaren gidan matan, suna ajiyewa.
“Ba a jima ba sai ga wuta daga inda ake kwasar man kuma muna kyautata zaton cewa gogayyar bokiti ne da daben siminti ya haddasa kasancewarta, domin bayan fara tsiyayar man nan an bi dukkan wuraren girke-girke an kashe wutar.”
A zantawarsa da Aminiya, wani limamin masallacin Juma’a da ke daura da inda tankar ta kafe, mai suna Malam Muhammad Rabi’u Abdullahi, ya ce bayan kula da fara tsiyayar man, sun yi saurin daukar matakin hana ajiye mai a jikin masallacin da kuma bacocin da ke kusa da shi. Ya ce masu motoci sun hanzarta janye motocinsu daga jerin gwanon inda hakan ya taimaka wajen magance aukuwar gobara ta bangaren.
Wasu da lamarin ya faru a gabansu sun bayyana cewa akwai kananan motoci biyu da ke gaban tankar da aka buga da suka samu lahanin karo, amma sai suka kara gaba tare da tankar da ke bayansu bayan sun kula da tsiyayewar mai daga tankar da lamarin ya faru da ita. Sun ce “Tankar ta kama wuta tare da wata motar bas da wata karamar mota da kuma wata babbar mota da aka ajiye su a mabanbantan wurare, don yi masu gyara.
Jam’an ’yan kwana-kwana sun samu nasarar kashe wutar bayan awa biyu tana ci, sannan aka garzaya da wadanda suka samu raunuka zuwa asibitocin Umaru Musa ’Yar-aduwa da ke garin Sabo-Wuse da babban asbitin Suleja sai kuma asibitin koyarwa na Jami’ar Abuja da ke Gwagwalada. Haka nan akwai wadanda aka kai wani wajen aikin gargajiya a garin Suleja, a yayin da wasu kuwa aka wuce da su zuwa garuruwansu, kuma daga wadannan bangarorin ne aka rika samun labarin karin adadin mutuwar bayan adadin da aka samu rana ta farko.
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Elrufa’i ya ziyarci garin da ke yankin karamar Hukumar Kagarko a ranar Lahadin da ta gabata, inda ya jajanta wa al’ummar yankin tare da jaddada aniyar gwamnatinsa na karasa aikin garejin manyan motoci a garin da ta faro bayan jingine aikin na tsawon shekaru.
Babban jami’in ’yan sanda na garin Tafa, CSP Faruk Umar wanda ya tabbatar da faruwan lamarin, ya bayyana cewa bai da ikon yin bayani a kan lamarin sai dai ya ce ya mika rahotonsa ga rundunar ’yan sanda ta jihar bayan kwamishinan ’yan sanda na jhar ya ziyarci yankin tun a ranar da lamarin ya faru.