Gobarar tukunyar gas tayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a Kaduna
Mutane da dama sun rasa rayukan su bayan fashewar tukunyar gas a unguwar Sabon Tasha da ke Kaduna a yau Asabar da misalin karfe 1:00 na rana. Lamarin ya faru ne a wani shago da ke kallon gidan man fetur na Total da ke Sabon Tasha a jihar . Karar fashewar bututun gas din ya […]
Mutane da dama sun rasa rayukan su bayan fashewar tukunyar gas a unguwar Sabon Tasha da ke Kaduna a yau Asabar da misalin karfe 1:00 na rana. Lamarin ya faru ne a wani shago da ke kallon gidan man fetur na Total da ke Sabon Tasha a jihar .
Karar fashewar bututun gas din ya razana mutane da gidajensu ke kusa da wurin inda su kayi tsamanin fashewar bam ne ko harin Boko Haram.
Wani da fashewar gas din ya faru a gabansa me suna Philip Kambai, wanda yana daya daga cikin wanda ya tsira daga fashewar bam din ya shaidawa cewa yana cikin wani shagon aski ne da ke kusa da shagon sayar da gas din tare da wasu mutane uku da suka zo yin aski a lokacin da abin ya faru.
Philip, ya ce “Ina hanyar fita bayan an gama min aski ne lokacin da na ji kara bam! Na fadi kasa amma na tashi da kyar na haura katanga garin hakan na ji rauni. Wani mutum shima ya haura katangar amma bana tsammanin mai askin da sauran mutane biyun sun fito.” Fashewar gas din ya tarwatsa jikin wadanda suka rasu.
