Gobe ake fara zabubbuka: Allah Ya sa a yi lami lafiya

Allah cikin ikonSa da falalarSa, gobe Asabar in Allah Ya so hukumkar zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC, za ta fara gudanar da zabubbukan bana. Zabubbkan da mutanen kasar nan sama da miliyan 60, da suka cancanci kada kuri`a, za su bazama zuwa tashoshin zabe kusan 120,000, don fara kada kuri`unsu a kan […]

Gobe ake fara zabubbuka: Allah Ya sa a yi lami lafiya
Gobe ake fara zabubbuka: Allah Ya sa a yi lami lafiya

Allah cikin ikonSa da falalarSa, gobe Asabar in Allah Ya so hukumkar zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC, za ta fara gudanar da zabubbukan bana. Zabubbkan da mutanen kasar nan sama da miliyan 60, da suka cancanci kada kuri`a, za su bazama zuwa tashoshin zabe kusan 120,000, don fara kada kuri`unsu a kan masu neman Shugabancin kasa da kuma na Majalisun Dokoki na kasa, wato ‘yan Majalisar Dattawa da ‘yan Majalisar Wakilai. Yayin da a ranar 11 ga watan Afrilun ‘yan kasar, Hukumar ta INEC kan shirya irin wannan babban zabe duk bayan shekaru hurhuda, tun da aka dawo mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999.

A da dai, hukumar ta INEC ta shirya gudanar da zabubbukan banan ne a ranakun 14 da 28 ga watan Fabrairun da ya gabata, amma haka kwatsam a ranar 6 ga watan na Fabrairu sai hedkwatar rundunar tsaro ta kasa ta shawarci hukumar da lalle ta dage gudanar da zabubbukan akalla sati shida, bisa ga hanzarin cewa za ta fara yaki gadan-gadan da `yan tada kayar bayan kasar nan a shiyyar Arewa maso Yamma, wato `yan kungiyar Boko Haram da suka shafe kusan shekaru shida suna cin karensu ba babbaka a jihohi irin su Barno da Yobe da Adamawa da wasu jihohin Arewa, bisa ga hanzarin cewa sojoji da za su bayar da kariya a ikin zabubbukan ba za su samu sukunin yin haka ba saboda za su kasance a filin dagar.
Wannan dage zabubbukan bisa ga umurnin hedkwatar tsaron kasar, ta janyo kace-nace, tsakanin `yan jam`iyyar adawa ta APC da jam`iyyar PDP da ma sauran `yan kasa, ta yadda wasu suka rika cewa jam`iyyar PDP da shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan suka shirya wa sojojin wannan kutu-kutu don kawai sun hango ba su da nasara a cikin zabubbukan, suna masu cewa yaushe sojojin da suka kasa kawo karshen wannan annoba a cikin shekaru shida, za su iya kawo karshenta a cikin makonni shida. Jam`iyyar PDP da shi kansa shugaba Jonathan da wasu magoya bayansa sun ta musanta wadancan zarge-zarge, suna masu cewa hukumar INEC ce ba ta shirya yadda ya kamata ba,suna masu zargin cewa a lokacin masu kada kuri`a kashi 56 cikin 100 ne kadai suka samu katin kada kuri`unsu na din-din-din. Alhali tun a wancan lokacin shugaban hukumar INEC din Farfesa Attahiru Jega ya sha nanata cewa hukumarsa ta shirya tsaf don gudanar da wannan gagarumin aiki.
Maganar da ake ciki yanzu rahotanni sun tabbatar askarawan kasar nan da taimakon sojojin hadin gwiwa daga kasashen Jamhuriyar Nijar da Benin da Kamaru da Chadi, sun kwato kusan dukkan hedkwatocin kananan hukumomi sama da 20, da kauyukan da `yan kungiyar ta Boko Haram suke kame tun a shekarar bara jihohin Adamawa da Yobe da Barno, in banda wasu hedkwatocin kananan hukumomi uku na jihar Barno ciki kuwa har da hedkwatar karamar hukumar Gwoza inda `yan kungiyar suka mayar hedkwatar daularsu.
A kan batun rabon katuttukan zabe na din-din-din kuwa tun kusan makonni biyu da suka gabata, Kakakin shugaban hukuamar zaben Mista Kayode Idowu ya fada wa wani taron manema labarai a Abuja cewa zuwa ranar 12 ga wannan watan, aikin rabon katututtun kada kuri`un na din-din-din ya kai kashi 81.2 cikin 100. Mai karatu, sai ka kaddara zuwa ranar Lahadin wannan makon da hukumar ta INEC ta rufe shirin karbar katuttukan kada kuri`un na din-din-din kashi nawa ta cimma nasarar rabawa a cikin kasa?
A dai cikin wannan karin lokacin ne hukumar ta INEC, ta samu damar jarraba na`urar tantance masu kada kuri`a a wasu mazabu na jihohi sha biyu da aka zaba daga shiyyoyi shidda na kasar nan, gwajin da sai dai a ce son barka, don kuwa ya kawar da shakku daga zukatan wasu masu kada kuri`u na kasar nan a kan yadda za a yi aiki da shi, da yadda zai rage ko ma ya hana magudin zabe kwata-kwata, kamar yadda aniyar bullo da amfani da shi tun farko ta tanada. Yayin da ya kara jefa shakku ga zukatan wadanda dama suke da adawa da yin amfani da shi din, don zai toshe masu kofofin yin magudin zaben da suka saba yi.
Zaben na bana, zabe ne da ba wai `yan kasa kadai ba, suka zuba masa ido ba a kan yadda zai kaya, a`a hatta mahukunta da kungiyoyin kasashen waje su ma sun zuba masa ido, bisa ga irin yadda suke son a rika yin sahihi kuma karbabben mulkin dimokuradiyya, wanda ta hanyar sahihin zabe kadai ake samunsa a ko ina. Mutanen kasa da ma na wajen sun kuma zura idanu ne a kan zaben kasar nan saboda muhimmancin da kasar take da shi a idanun duniya, ba wai a nahiyar Afirka kadai ba. Dadin dadawa a bana a ciki da waje ana tsammanin samun CANJI a gwamnatin tsakiya. Alal misali wata babbar cibiyar kasa da kasa mai nazari a kan harkokin siyasa da ke birnin London, wato Eurasia Group, kwanannan ta canja rahoton sakamakon bincikenta na jin ra`ayin jama`ar kasar nan da ta fitar a cikin watan Agustan bara da ya tabbatar mata cewa, shugaba Jonathan shi zai lashe zaben. A wani sabon rahotan da ta fitar a Asabar din wancan makon ta tabbatar da cewa Janar Muhammadu Buhari na jam`iyyar adawa ta APC, shi zai lashe zaben in Allah ya so da kashi 60 cikin 100.
A nan cikin gida ma, wata kungiya mai suna Allience for Credible Election (ANE- Negeria), a rahotanta da ta fitar a cikin makon jiya, bayan tuntubar jin ra `ayoyin jama`a ta wayar tarho da ta yi tsakanin 23 zuwa 27 ga watan Fabrairun da ya gabata,ita ma ta tabbatar da cewa kashi 44 na jama`ar da ta tuntuba sun ce za su zabi Janar Buhari, yayin da kashi 36, suka ce za su zabi shugaba Jonathan, kashi 19, suka ki su ba da amsa, yayin da kashi 1, suka yi jemage.
Zaben banan dai ya yi matukar shan bamban da wadanda suka rigaye shi na shekarun 1999, da 2003, da na 2007 da na 2011, ba wai don zazzafan yakin neman zaben rura wutar bambancin kabilanci da na addini da jinsi da ake yi ba, duk kuwa da sa hannun tabbatar da zaman lafiya kafin zabe da lokacin zabe da ma bayan zaben da jami`an tsaro suka rika sa dukkan `yan takara suna sa hannu a kai, tun daga sama har kasa, a` a sai don irin yadda bayanai a cikin gida da waje (kamar yadda na kawo su a sama), suke karfafa cewa ba makawa jam`iyyar PDP, za ta sha kayi a cikin takarar neman shugabancin kasa. Kayin da zai iya zama na farko irinsa `jam`iyyar adawa ta karbi mulki a cikin mulkin dimokuradiyyar da ake kai yau shekaru 16.
Duk da shugaba Jonathan da mukarraban jam`iyyarsa na PDP suna ta nanata babu aniyar kafa gwamnatin rikon kwarya, amma dai `yan adawa sun dage a kan cewa wannan boyayyiyar aniya ta gwamnatin tarayya tana nan, duk kuwa da ba tanadin haka a cikin kundin tsarin mulkin kasar nan.
Daga irin yadda aka kada wannan garwa a wannan karo, wanda ya fi fitowa daga jam`iyyar PDP mai mulkin, da irin kayan aiki (kudade) da ake zargin tana rabawa ga magoya baya da malaman manyan addinan kasar nan biyu, da irin barazanar idan har shugaba mai ci bai yi nasara da ake samu daga wasu `yan kabilarsa ta Neja Delta, to , kuwa za a yi yaki. Ba abin da ya fi alheri da ya wuce a ci gaba da addu`ar Allah ya sa a yi zabe lami lafiya, ya kuma ba mu ikon zaben shugabanni na gari amin summa amin.