Gobe ake taron Gizagawan Najeriya a Katsina
A gobe Asabar da misalin karfe 10 na safe, ake bude gagarumin taron Gizagawan Najeriya kashi na biyar a zauren taro na Multi Purpose Conference Hall a Filin Samji Katsina Taron na kwana biyu, za a fara gudanar da shi ne tun daga yau da dare, inda za a nishadantar da mahalarta taron da wasannin […]
A gobe Asabar da misalin karfe 10 na safe, ake bude gagarumin taron Gizagawan Najeriya kashi na biyar a zauren taro na Multi Purpose Conference Hall a Filin Samji Katsina
Taron na kwana biyu, za a fara gudanar da shi ne tun daga yau da dare, inda za a nishadantar da mahalarta taron da wasannin gargajiya. Sai kuma a ranar Asabar, inda za a gabatar da babban jawabi mai taken, “Annobar Shaye-Shayen Miyagun kwayoyi A Tsakanin Matasa: Ina Mafita?”
Babban bako na musamman, wanda kuma za a yi wa karramawa ta musamman, shi ne Babban Jojin Jihar Katsina, Mai shari’a Musa danladi Abubakar (NPOM). A yayin da Shugaban taron zai kasance Alhaji Khalil Ibrahim Aminu, Mai ba Gwamnan Jihar Katsina Shawara Kan Al’amuran Matasa.
Uban taro kuwa, shi ne Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk (CON). Sai Babban Bako Mai jawabi, Alhaji Ibrahim Katsina. A yayin da Dokta Bashir Usman Ruwan Godiya, Mai ba Gwamnan Jihar Katsina Shawara Kan Ilimi Mai Zurfi, zai kasance mai sharhi kan takardar da za a gabatar.