Gobe APC za gana kan Shugabancin Majalisar Dattawa
Gobe Asabar ne Jam’iyyar APC za ta gana don yanke shawara kan wanda za a gabatar a matsayin dan takara daya tilo na shugabancin Majalisar Dattawa. A jiya Alhamis ne jam’iyyar ta shirya zama a tsakanin Babban Kwamitin Gudanarwarta (NWC) da zababbun ’yan majalisar, kafin ta dage zuwa gobe.Akwai bayanan da suka nuna cewa hankalin […]
Gobe Asabar ne Jam’iyyar APC za ta gana don yanke shawara kan wanda za a gabatar a matsayin dan takara daya tilo na shugabancin Majalisar Dattawa.
A jiya Alhamis ne jam’iyyar ta shirya zama a tsakanin Babban Kwamitin Gudanarwarta (NWC) da zababbun ’yan majalisar, kafin ta dage zuwa gobe.
Akwai bayanan da suka nuna cewa hankalin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fi kwantawa da Sanata Ahmed Lawan a lokacin da ya gana da wakilan babban kwamitin jam’iyyar a ranar Talatar da ta gabata.
Majiyoyi da dama a wurin taron sun ce Buhari ya nuna ya fi aminta da Sanata Lawan ne wanda ya fito daga Jihar Yobe saboda kwarewa da gogewa da kuma rikon amanarsa.
Tuni alamu suka nuna cewa akwai yiwuwar Jam’iyyar APC ta amince da Sanata Ahmed Lawan a matsayin dan takara daya a kan mukamin, tare da sa ran wakilan majalisar su zabe shi a ranar Talata mai zuwa.
Sanata Lawan wanda ke fuskantar babban kalubale daga Sanata Bukola Saraki da ya fito daga Jihar Kwara a Arewa ta Tsakiya, ana ganin ya cika wasu sharudda da Jam’iyyar APC ta gindaya da suka hada da kasancewa tsohon hannu a majalisar da rashin samunsa ko tuhumarsa da wata almundahana, sai kuma matsayar da aka ce an cimmawa ta tura kujerar ga yanki na biyu da ya fi ba Jam’iyyar APC kuri’a a zaben da ya gabata, wanda hakan na nufin yankin Arewa maso Gabas ne. Sannan kujerar ta dade a yankin Arewa ta Tsakiya na tsawon shekaru.
Tun a shekaranjiya Laraba ne alamu suka nuna cewa akwai yiwuwar Sanata Ahmed Lawan ya zama Shugaban majalisar bayan taron na Babban Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar APC da Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata da daddare.
Sanata Lawan ya kasance a majalisa tun 1999, yayin da babban mai kalubalantarsa Sanata Bukola Saraki, ya shekara hudu, kuma ya fito ne daga Arewa ta Tsakiya, wadda ba ta bayar da kuri’un da Arewa ta Gabas ta ba APC ba.
Mako biyu da suka gabata wata kungiyar da ake aiki don a zabi Sanata Bukola a matsayin shugaban majalisar mai suna Like Minds ta tara sunayen sanatocin APC 34 da ta ce sun amince da takararsa. Sai dai jim kadan da fitar da wannan bayani, kungiyar Unity Forum ta sanatocin da ke goyon bayan Sanata Lawan ta yi da’awar cewa sanatocin APC 40 sun amince da takararsa. Ana jin wannan tankiya na daga cikin dalilan dage zaman da aka shirya a jiya Alhamis zuwa gobe.
Shugaba Muhammadu Buhari ya riga ya ce zai yi aiki da duk wanda ya zama shugaban majalisar dattawa ko ta wakilai. “A shirye nake in yi aiki da duk wanda ya zama shugaban majalisar tarayya ko ta dattawa, ban damu daga inda ya fito ko ta fito ba. Akwai ka’idojin da ake bi wajen zaben shugabannin majalisar kuma ba zan yi karan-tsaye ga ka’idojin ba,” inji Buhari.
Akwai masu tsoron cewa matsayin APC na amfani da wadancan ka’idoji da suke jin baki ne a dokokin majalisar dattawa da tsarin mulki na iya jawo mata matsala, musamman da yake babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta yi kwanton bauna tana jira a samu baraka a APC don ta ci ribar haka wajen cimma wasu manufofinta.