Gobe Arsenal za ta hadu da Aston billa a kofin FA yayin da FC Barcelona kuma za ta kece raini da Atletic Bilbao a kofin Copa Del Rey

A gobe Asabar, 30 ga Mayu ne ake sa ran kungiyar kwallon kafa ta Arsenal za ta hadu da Aston billa a wasan karshe na cin kofin kalubale na Ingila (FA Cup). Za a fara wasan ne da misalin karfe biyar da rabi na yamma agogon Najeriya a filin wasa na Wembley da ke Ingila.Arsenal […]

Gobe Arsenal za ta hadu da Aston billa a kofin FA yayin da FC Barcelona kuma za ta kece raini da Atletic Bilbao a kofin Copa Del Rey
Gobe Arsenal za ta hadu da Aston billa a kofin FA yayin da FC Barcelona kuma za ta kece raini da Atletic Bilbao a kofin Copa Del Rey

A gobe Asabar, 30 ga Mayu ne ake sa ran kungiyar kwallon kafa ta Arsenal za ta hadu da Aston billa a wasan karshe na cin kofin kalubale na Ingila (FA Cup).

Za a fara wasan ne da misalin karfe biyar da rabi na yamma agogon Najeriya a filin wasa na Wembley da ke Ingila.
Arsenal ce ke rike da kofin don haka idan ta samu nasara za ta kafa tarihi a matsayin kungiyar da take rike da kofin kuma ta sake daukarsa a jere ba tare da ta huta ba. Sai dai da wuya dan kwallon gaban Arsenal Danny Wellbeck ya yi wasan saboda raunin da yake fama da shi.
Haka kuma a gobe ne ake sa ran kulob din FC Barcelona da ke Sifen zai hadu da na Athletico Bilbao a wasan karshe na cin kofin kalubalen Sifen da aka fi sani da Copa Del Rey.
Wasan zai gudana ne da misalin karfe 8 na dare agogon Najeriya. Wannan shi ne kofi na biyu da FC Barcelona take hankoron lashewa a bana daga cikin kofuna ukun da take zawarci. dan wasan gaba na Barcelona Luis Suarez da wuya ya buga wasan saboda raunin da ya samu kuma ana ganin da wuya ya murmure kafin wasan. Tuni Barcelona ta lashe kofin La-Liga na Sifen a karshen makon da ya gabata. A ranar 6 ga watan gobe ne kuma za ta kece raini da kulob din Jubentus na Italiya a wasan karshe na gasar zakarun kulob-kulob na Turai watau UEFA Champions League.
A zamanin tsohon kocin Barcelona, Pep Guardiola ne kulob din ya taba lashe kofunan La-Liga da na Copa Del Rey da kuma na Champions League a kakar wasa daya. Don haka a wannan karo ma akwai yiwuwar hakan ta sake faruwa a karkashin horarwar Luis Enrikue, kocin FC Barcelona na yanzu.
Sai dai shi ma kulob din Jubentus na Italiya ba kanwar lasa ba ne, don tuni ya lashe kofuna biyu a bana kuma yake hankoron lashe na ukun. Ya lashe kofin kalubale na Italiya (Italian Cup) a makon jiya sannan kulob din ne ya lashe gasar rukuni-rukuni na kasar da ake wa lakabi da Serie A kimanin makonni uku da suka wuce sannan yanzu kuma ya karkara akalarsa ne don ganin ya samu nasara a wasan karshen da za su gwabza da Barcelona a kofin zakarun kulob-kulob na Turai (Champion League) a wasan za zai gudana a filin wasa na Berlin da ke Jamus a ranar 6 ga watan gobe.