Gobe Gwamna Suntai zai dawo – Matarsa
Uwargidan Gwamnan Jihar Taraba Misis Hauwa danbaba Suntai ta ce, ana sa ran mijinta Gwamna danfulani danbaba Suntai zai bar asibitin Sea biew Hospital Rehabilitation Centre and Home da ke birnin New York domin komowa Najeriya a gobe Asabar.Matar Gwamnan ta bayyana haka ne a tattaunawarta da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ta wayar […]

Uwargidan Gwamnan Jihar Taraba Misis Hauwa danbaba Suntai ta ce, ana sa ran mijinta Gwamna danfulani danbaba Suntai zai bar asibitin Sea biew Hospital Rehabilitation Centre and Home da ke birnin New York domin komowa Najeriya a gobe Asabar.
Matar Gwamnan ta bayyana haka ne a tattaunawarta da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ta wayar tarho a birnin New York a ranar Talatar da ta gabata.
Ta ce an kammala dukkan shirye-shiryen da suka kamata domin dawowar Gwamnan, wanda ya shafe watanni a asibitin, sakamakon raunin da ya samu bayan da jirginsa ya yi hadari ya fado kasa a watan Oktoban bara a Jihar Adamawa.