Gobe Jami’ar ABU za ta karrama marubuci Dokta Bukar Usman da malaminsa Ali Monguno

A gobe Asabar, Jami’ar Ahmadu Bello Zariya za ta karrama fitaccen marubuci kuma tsohon Babban Sakatare a fadar Shugaban kasa, Dokta Bukar Usman da digirin girmamawa (Doctor of Letters). Marubucin zai karbi digirin girmamawar ne a wurin bikin yaye dalibai karo ma 37 da zai gudana a jami’ar. Shi kansa tsohon dalibin jami’ar ne, inda […]

Gobe Jami’ar ABU za ta karrama marubuci Dokta Bukar Usman da malaminsa Ali Monguno
Gobe Jami’ar ABU za ta karrama marubuci Dokta Bukar Usman da malaminsa Ali Monguno

A gobe Asabar, Jami’ar Ahmadu Bello Zariya za ta karrama fitaccen marubuci kuma tsohon Babban Sakatare a fadar Shugaban kasa, Dokta Bukar Usman da digirin girmamawa (Doctor of Letters).

Marubucin zai karbi digirin girmamawar ne a wurin bikin yaye dalibai karo ma 37 da zai gudana a jami’ar. Shi kansa tsohon dalibin jami’ar ne, inda ya kammala karatunsa na digirin farko a fannin sha’anin mulki a 1969. Ya gudanar da aikace-aikacen gwamnati, inda har ya kai mukamin Babban Sakatare a fadar Shugaban kasa, inda ya yi ritaya a 1999. Ya tsunduma harkar rubuce-rubuce da Ingilishi da kuma Hausa, inda ya zuwa yanzu ya wallafa littattafai sama da ashirin, baya da kuma gidauniyar tallafa wa al’umma da ya kafa mai suna Bukar Usman Foundation.
A wata tattaunawa da ’yan jarida, Shugaban Jami’ar ABU, Farfesa Abdullahi Mustapha ya bayyana dalilin da ya sanya hukumar jami’ar ta yanke kudurin karrama marubuci Bukar Usman, wanda haifaffen garin Biu ne da ke Jihar Borno da kuma malaminsa, tsohon Ministan Fetur da Makamashi, Alhaji Shettima Ali Munguno da kuma Yarima Talal Abdul’azeez Bin al-Saud, dan kasar Saudi Arebiya. Shugaban jami’ar ya ce cancanta suka duba da kuma hidimar da mutanen suke wa jama’a a fannonin rayuwa daban-daban ta sa aka zabe su domin karrama su.
Aminiya ta tambayi Bukar Usman, ko yaya ya ji da ya samu takarda daga jami’ar cewa za a karrama shi da wannan digiri na girmamawa? Sai ya amsa da cewa: “Babu abin da zan ce da ya wuce in yi godiya ga Allah da Ya raya ni kuma Ya ba ni ikon tafiyar da rayuwa, har ta kai ga an ga muhimmancin abin da nake yi kuma muhimmiyar jami’a kamar ABU ta karrama ni. Haka kuma ina godiya ga mutanen da suka duba cewa na cancanci a ba ni wannan karimci, suka zabe ni a matsayin daya daga cikin wadanda za a karrama.”
Ya ci gaba da cewa: “Wani abin da ya kara mani farin ciki da wannan karramawa shi ne, yadda aka hada ni da muhimmin mutum, Malam Shettima Alu Monguno. Shi malamina ne a lokacin da nake makarantar sakandare a Maiduguri kuma na yi aiki a karkashinsa a Ma’aikatar Ma’adinai da Makamashi ta Gwamnatin Tarayya. Mutum ne shi mai gaskiya da amana. A lokacin nan, idan aka ba shi kudin zuwa wani taro zuwa wata kasa, idan ya dawo ko kwabo ya rage sai ya maido shi. Abin da ya koya mana ke nan, gaskiya da amana. To, yau a ce za a karrama ni tare da shi, wannan abin farin ciki ne kuma abin alfahari ne. Ina godiya ga Allah kuma ina godiya ga mutanen da suka zabe mu a wannan karramawa.”
A bana shekarun Bukar Usman 71 a duniya, an tambaye shi cewa wane bambancin rayuwa ya samu a yanzu da kuma kafin ya kawo wannan lokacin? Shi kuwa ya amsa da cewa: “To gaskiya shekaru saba’in da dayan da na yi, talatin daga cikinsu na yi su ne a aikin Gwamnatin Tarayya, wanda wannan shi ne bangare mafi yawa yayin girmana. Don haka cewa yaya na ji, akasari ya ta’allaka ne da kasancewata ma’aikacin gwamnati har zuwa lokacin da na yi ritaya a shekarar 1999. Na sha fada a baya cewa, addu’ata a kullum ita ce na bar aiki a lokacin ina da sauran karfi da zan iya amfanar kaina kuma Allah Ya amsa addu’ata a lokacin da ya dace. Na ce lokacin da ya dace saboda na bar aiki a watan Afrilun 1999, duk da cewa a shirye nake na tafi, sai aka ce na yi ritaya bayan an ba ni wa’adin wata daya. Ba wai kora ta aka yi ba, a’a ina kyautata zaton cewa gwamnati tana bukatar gurabe don saka wasu, don haka sai suka shiga lalube har aka gano wasu daga cikinmu wadanda muna kan mukamin manyan sakatarori kusan shekaru goma sha daya, aka ce ya kamata na je na huta.
“Saboda haka a karshen watan Afrilu na shekarar 1999 sai na yi ritaya. Abu na farko da ya girgiza ni shi ne cewa ni nake daukar nauyin komai nawa: Biyan kudin hayar gida, kula da motoci da kuma rasa duk wasu damammaki da jami’in gwamnati mai mukamin darakta zuwa sama kan samu. Na yi kokarin sabawa da yanayin da na tsinci kaina a ciki, saboda na farko dai ba ni da direba, a da ina da guda biyu daya bayan daya shekaru uku da yin ritayata amma daga baya sai na sallame su, na zauna ba ni da direba. Idan ina so na bar Abuja sai na yi hayar motar da za ta kai ni. Ya zamana ni da maidakina mu muke tuki da kanmu. Saboda haka rayuwa bayan aiki zan iya cewa akwai nauye-nauyen kula da gida ta yadda kowanne lokaci za ka biya al’amuran kula da gidan duk da cewa yanzu gwamnati kudi take bayarwa kan wasu abubuwa kamar harkar gida da wasu hakkokin ma’aikata amma duk da haka abin da nake biya a gidan gwamnati dan kankani ne idan an kwatanta da abin da nake biya yanzu.”
Ya ci gaba da bayyana cewa: “Ba shakka shigata harkar rubuce-rubuce ta yi karfi ne bayan na bar aiki. Mutane sukan yi bikin taya murna idan sun kai shekaru 70 a raye, amma ni ban yi ba. Dalili kuwa shi ne na fahimci cewa mutane sun dauki abin kamar wani abu ne na kasaita da nuna isa amma ni ko a gidana babu wani bikin taya murna da aka yi. Nakan fada wa mutane cewa ban taba yin bikin murnar ranar zagayowar haihuwata ba tun daga lokacin da na fara sanin wani abu a rayuwa har zuwa cika shekaru 69, saboda haka shekaru 70 haka suka zo min. Don haka sai na dauki abin kamar yadda nake gudanar da rayuwata, ba wani abu daban ba. Amma duk da haka masu yi min fatan alheri sun dauki hakan a matsayin abin da ya cancanta a shirya bikin taya murna a kai, saboda haka wasu daga cikin abokaina har da kai kuka yi wani abu. Ina gode wa Allah kasancewata yau ina da shekaru saba’in da rabi a duniya. Kai wa shekara 70 na nufin ka fara tattara komatsanka; Allah Ne kadai Ya san ranar da mutum zai mutu, amma fa mutane kadan ne suke kaiwa wadannan shekarun cikin ingantacciyar lafiya da kwanciyar hankali. Saboda haka ina matukar godiya ga Allah.”
Da aka juya ta bangaren rubuce-rubucensa, an tambaye shi cewa, ya rubuta littattafai sama da guda ashirin a cikin shekaru bakwai, mene ne sirrin haka kuma ta ina ya samu kwarin jiki ko karfin gwiwar yin haka?
Dokta Bukar ya ce: “karfin gwiwar daga al’umma ne. Daga cikin littattafaina guda ashirin, da yawansu da harshen Hausa na rubuta, wato littattafan tatsuniyoyi. Bayan na rubuta tarihin rayuwata, Hatching Hopes da boices in a Choir, sai masu buga min littattafai suka tambaye ni “wai ba ka da wasu abubuwa ne?” Saboda haka daga wannan lokacin sai na karkatar da tunanina kan tatsuniyoyi, ta wannan hanya na samo sha’awar rubutu. Suna tambaya ta “wai ba ku da wasu labarurruka daga yankinku da za ka bayyana ne?” Nan da nan sai tunanina ya hararo tatsuniyoyin da mahaifiyata da wasu mutanen suka fada min lokacin ina karami. Sai na tuna cewa al’adar fadin tatsuniya da baki tana mutuwa, tsofaffin da suke fada wa yara tafiya suke yi, su kuma matasa abin da suka fi mayar da hankali shi ne kallon talabijin da littattafai da shirye-shiryen da suke zuwa daga kasashen ketare. Da wahala ka ga yaranmu na yanzu suna amfana da abubuwan da muka samu a shekarar 1950. Wannan dalili shi ya karfafa min gwiwar shiga fagen tatsuniyoyi. Na fada wa mutane cewa tatsuniyoyi fagena ne kuma a kasa irin Nijeriya mai yarurruka da kabilu sama da dari biyu da hamsin, fagen ne wanda ba shi da iyaka.”
Sannan kuma ya kara da cewa: “Zuwa yau da muke wannan tattaunawar, na tattara tatsuniyoyi daga Yarabawa, daga Ibo, daga Kudu maso kudu sama da guda dubu. Haka kuma muna nan muna kokarin tattaro na jihohin Kogi da Nasarawa da Binuwai da Neja da Filato, kai har da na babban birnin tarayya wato Abuja. Hakika mun samo na Hausa sosai kuma fagen yana da fadi kwarai da gaske. Wadannan su ne dalilan da suka zaburar da ni.
“Amma a bangaren littattafan aikin gwamnati da tsare-tsarenta kuwa, na yi imanin akwai tsare-tsare masu tarin yawa wadanda ya kamata mutane su sani. Na dauki kasancewata a aikin gwamnati na sama da shekara talatin a matsayin kalubalen da ya wajaba a kaina na yi rubutu a kan manufofi da tsare-tsaren gwamnati. Kuma bayanan da nake samu daga mutane ya kara min kwarin gwiwar rubuta su da yawa har zuwa lokacin da na ga ya kamata na tsagaita rubuta a jaridu na mayar da hankalina kacokan wajen ci gaba da rubutun littattafaina guda uku wato: Tarihin kasar Biu da bacewar Harshe da Mabanbantan Al’adu A Masarautar Biu da kuma Ilimin ’Ya’ya Mata a Masarautar Biu a Shekarun Farko. Guda biyu na karshe al’amari ne da yake faruwa a duniya baki daya, amma sai na karkatar da shi ta yadda zan fi samun zarafin fuskantar da al’amarin domin mu kalli abin ’yar cikin gida wato a matsayin abin da ya shafe mu domin mu fi tattauna shi sosai. Wannan shi ne abin da na sanya a gaba a halin yanzu.”

Yunwa da gazawar gwamnati ne sanadin turmutsutsi wajen rabon abinci — Kukah

Abba El-Mustapha ya samu lambar yabo kan yaƙi da cin hanci

Mahaifiyar Gwamnan Jigawa ta rasu

Najeriya ba ta cikin ƙasashen da suka fi cin bashi a Afirka – IMF