Gobe Jami’ar Ahmadu Bello za ta yaye dalibai dubu 17
Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta shirya domin gudanar da bikin yaye dalibanta karo na 38 a gobe Asabar, inda dalibai sama da dubu 17 za su karbi takardun shaida a fannoni daban-daban, daga tsangayoyi 12 da ke jami’ar.Shugaban Jami’ar Farfesa Ibrahim Garba ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da ’yan jarida a […]
Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta shirya domin gudanar da bikin yaye dalibanta karo na 38 a gobe Asabar, inda dalibai sama da dubu 17 za su karbi takardun shaida a fannoni daban-daban, daga tsangayoyi 12 da ke jami’ar.
Shugaban Jami’ar Farfesa Ibrahim Garba ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da ’yan jarida a harabar jami’ar da ke Samaru, Zariya.
Farfesa Ibrahim Garba ya ce fitaccen dan kasuwar nan Alhaji Aliko dangote zai gabatar da kasida a taron da zai gudana yau Juma’a, inda Mai martaba Sarkin Kano, Malama Muhammadu Sanusi na Biyu zai shugabanci taron, daga bisani a baje kolin fasahar zane-zane da daliban jami’ar suka yi a kan tarihin Masarautar Kano.
Daya ke tsokaci a kan nasarorin da jami’ar ta samu a shekarun bayan nan, shugaban ya yi bayani a kan motar da fannin injiya na jami’ar ya kirkiro da karbuwar da ta samu a kasashen duniya, kuma ya ce sun samu nasarar kirkiro da wata karamar matatar man fetur da kuma wata na’ura mai amfani da hasken rana wajen samar da wutar lantarki.
Ferfesa Ibrahim Garba ya koka kan rashin muhallin ga dakibansu, yana mai cewa a cikin daliban jami’ar dubu 40, a yanzu dalibai dubu 12 ne kawai suke iya samun dakunan kwana a harabar jami’ar, “Hakan na tsananin tayar mana da hankali kuma mun dukufa wajen ganin mun magance matsalar,” inji shi.