Gobe mutanen Jihar Osun za su yi zaben Gwamna

Bayan gudanar da manyan gangami da manyan jam’iyyun PDP da APC suka yi don fafatawa a zaben Gwamnan Jihar Osun, jama’ar jihar za su yanke hukunci a gobe domin zaben wanda suke so ya mulki jihar na tsawon shekara hudu.A wani gangami da APC ta kira Mega Rally a ranar Talata a garin Osogbo fadar […]

Gobe mutanen Jihar Osun za su yi zaben Gwamna
Gobe mutanen Jihar Osun za su yi zaben Gwamna

Bayan gudanar da manyan gangami da manyan jam’iyyun PDP da APC suka yi don fafatawa a zaben Gwamnan Jihar Osun, jama’ar jihar za su yanke hukunci a gobe domin zaben wanda suke so ya mulki jihar na tsawon shekara hudu.
A wani gangami da APC ta kira Mega Rally a ranar Talata a garin Osogbo fadar jihar domin yakin neman sake zaben Gwamna Rauf Aregbesola, daukacin jiga-jigan jam’iyyar da zababbun ’ya’yanta ciki har da tsohon Sakataren Jam’iyyar PDP na kasa kuma tsohon Gwamnan Jihar, Olagunsoye Oyinlola da ya koma jam’iyyar ne suka halarta.
Sauran wadanda suka halarci gangamin sun hada da jagoranta Cif Bola Tinubu da shugabanta na kasa, John Odigie-Oyegun da tsohon shugaban riko na kasa, Bisi Akande da tsohon Gwamnan Jihar Isiaka Adeleke da tsohon Gwamnan Jihar Kwara, Bukola Saraki da tsohon shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Abubakar Baraje, da tsofaffin gwamnonin Jihar Ekiti, Niyi Adebayo da Segun Oni.
Gwamna Adams Oshiomhole na Edo da Abiola Ajimobi na Oyo da Ibikunle Amosun na Ogun da Rochas Okorocha  na Imo da Kayode Fayemi  na Ekiti da Abdulfatah Ahmed  na Kwara da Mataimakiyar Gwamnan Jihar Legas, Adejoke Oorelope-Adefulire duk sun halarci gangamin.
Jam’iyyar PDP wadda ita ce babbar jam’iyyar adawa a jihar ta gudanar da naa gangamin ne a ranar Asabar da ta gabata, inda Shugaba Goodluck Jonathan da Maaimakinsa Namadi Sambo da shugabana na kasa Adamu Mu’azu suka halarta.
Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Cif Oyegun a bukaci Gwamnatin Tarayya a karkashin Jam’iyyar PDP da Hukumar Zabe ta kasa (INEC) su kyale jama’ar jihar su zabi wanda suke so a zaben gwamnan.
“A Osun, na ga soyaya da kauna ga Aregbesola. A Osun, na ga abin da ake da ke sa gwamna ya zama karbabbe. Ga wadanda suke da kunne ya kamata su ji cewa kada su yi wasi da ko kuri’a daya a Osun. Daga yanzu a shata fagen daga. APC ba za ta amince da duk wata gwamnati da sace zabin jama’a ba, wannan ba zai sake faruwa ba,” inji shi.
Shugaban APC din ya ce ’yan Najeriya suna son canji kuma “idan wani ya sace zabensu a zaben 2015, APC ba za ta amince da wannan gwamnati ba.”
Shi kuwa Cif Tinubu ya bukaci magoya bayan jam’iyyar ne da kada yawan jami’an tsaro da aka tura jihar ya firgita su, kuma ya nemi jami’an tsaron su yi aikinsu kamar yadda tsarin mulki ya nuna.
Gwamna Oshiomhole wanda ya yi magana a madadin gwamnonin APC ya ce nasarorin da Gwamna Aregebsola ya samu sun sanya tsoro a zukatan PDP da sauran ’yan adawa, inda ya bayyana Gwamnan da wakilin haske, yayin da sauran wakilan duhu.
Gwamna Aregbesola, wanda matarsa da mataimakiyarsa suka rufa wa baya, ya ce lokacin da Shugaba Jonathan ya jagoranci magoya bayan PDP zuwa Osun don gangami jama’ar jihar suna zaman makoki, amma sun kasance cikin murna a lokacin gangamin APC.
Sai dai a wata sanarwa da Kakakin PDP na kasa, Olisa Metuh ya fitar ya bayyana gangamin na APC da taron mutanen da aka yiwo hayarsu, inda ya ce an yiwo hayar mutane ne daga wasu jihohin APC aka tilasta su zuwa Osun don a nuna jam’iyyar da Gwamnan na da dimbin magoya baya. “Kuma muna tunatar da APC cewa al’ummar Jihar Osun ne kawai za su yi zabe ranar Asabar (gobe) ba dimbin jama’ar da ta yiwo haya ba,” inji shi.
Ya ce PDP tag ode wa al’ummar jihar kan goyon baya da hadin kai da suka nuna wa dan takararta, Iyiola Omisore.