Gobe Najeriya za ta kece raini da Sudan
A cigaba da fafatawa a gasar neman zuwa cin kofin Afirka da zai gudana a badi a kasar Maroko, kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles a gobe Asabar za ta yi tattaki zuwa Sudan don karawa a wasa zagaye na uku. Sannan a ranar Laraba mai zuwa watau 15 ga wannan wata nka Oktoba […]

A cigaba da fafatawa a gasar neman zuwa cin kofin Afirka da zai gudana a badi a kasar Maroko, kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles a gobe Asabar za ta yi tattaki zuwa Sudan don karawa a wasa zagaye na uku. Sannan a ranar Laraba mai zuwa watau 15 ga wannan wata nka Oktoba Sudan za ta biyo Najeriya gida don sake karawa. Najeriya dai ta hada maki daya ne kacal a wasanni biyu da ta yi. A wasan farko ta sha kashi ne a wajen Kongo da ci 3-2 a garin Kalaba a yayin da ta yi kunnen doki da Afirka ta Kudu a wasa na biyu. Ya zama tilas Najeriya ta samu nasara a wasanta da Sudan muddin tana son ta kai labari. Najeriya ce take rike da kofin Afirka bayan ta lashe shi a Afirka ta Kudu a shekarar bara don haka zai zama abin kunya idan ba ta kai labari ba a wannan mataki. Tuni wadansu masana harkar kwallo a Najeriya suka rika kiraye-kirayen a dauko sabon koci daga waje wanda zai iya tserar da kasar nan daga halin ni -’ya-sun da ta fada a fagen kwallo yayin da wasu kuma suke ganin idan aka yi haka ba a yi wa koci Stephen Keshi adalci ba ganin irin nasarorin da ya samu a baya. kasashe biyu ne watau na daya da na biyu a kowane rukuni ake sa ran za su haye gasar cin kofin Afirka a Maroko a badi. Yanzu dai Najeriya ce a matsayi na uku. Kongo ce ta farko sai Afirka ta Kudu sai Najeriya sai kuma ta karshe Sudan.