Gobe Super Eagles za ta kara da Tanzaniya
A gobe Asabar 5 ga Satumba ne ake sa ran kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta kece raini da ta Tanzaniya, a filin wasa na Dar el-Salam da ke Tanzaniya. Wasan zai gudana ne da misalin karfe 2 da rabi na rana agogon Najeriya.Wannan shi ne wasa na farko ga sabon kocin kungiyar […]
A gobe Asabar 5 ga Satumba ne ake sa ran kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta kece raini da ta Tanzaniya, a filin wasa na Dar el-Salam da ke Tanzaniya. Wasan zai gudana ne da misalin karfe 2 da rabi na rana agogon Najeriya.
Wannan shi ne wasa na farko ga sabon kocin kungiyar Sunday Oliseh tun bayan da Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) ta dauke shi aiki kimanin watanni biyu da suka wuce.
Idan za a tuna, wasan da kungiyar ta ta yi da Chadi ya gudana ne a garin Kaduna a watan Yunin da ya wuce kuma Super Eagles ce ta lallasa Chadi da ci 2-0. A wancan lokaci wasan ya gudana ne a karkashin kulawar tsohon kocin kungiyar Stephen Keshi. Sai dai jim kadan bayan wasan ne Hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) ta bayar da sanarwar korar kocin inda ta maye gurbinsa da Sunday Oliseh.
Wasan gobe zai yi zafi, musamman ganin yadda daukacin magoya bayan kungiyar suka zuba ido su ga yadda sabon kocin zai tunkari wasan. Najeriya tana bukatar lashe wasan ne don ta hada maki 6 a wasanni biyun da za ta yi.
Kawo yanzu Masar ce take gaban Najeriya a rukunin da maki uku da kwallaye uku bayan ta lallasa Tunisiya da ci 3-0 a wasan farko. Najeriya ke biye da maki uku da kwallaye biyu.
kasashe biyu ne ake sa ran za su haye gasar cin kofin Afirka da zai gudana a Gabon a shekarar 2017 daga kowane rukuni.