Gobe ‘yan takara zasu mayarwa INEC fom

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta ce gobe ne wa’adin da hukumar ta bayar don maida fom din takara na CF001 da CF002 daga jam’iyyun  kasar wato ‘yan takarar shugaban kasa da majalisar dokokin tarayya. INEC ta sanar da hakan ranar Alhamis data gabata ta bakin kwamishina kuma mamba a kwamitin  sadarwa […]

Gobe ‘yan takara zasu mayarwa INEC fom

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta ce gobe ne wa’adin da hukumar ta bayar don maida fom din takara na CF001 da CF002 daga jam’iyyun  kasar wato ‘yan takarar shugaban kasa da majalisar dokokin tarayya.

INEC ta sanar da hakan ranar Alhamis data gabata ta bakin kwamishina kuma mamba a kwamitin  sadarwa da ilmantar da masu zabe na hukumar INEC Malam Mohammed Haruna ya ce, hukumar ta bayar da wa’adin ranar 18 ga Oktoba don mayarwa INEC fom din takarar shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayyya yayin da ranar 2 ga Nuwamba ne ‘yan takarar Gwamnoni da na majalisun dokokin jihohi zasu mayar da nasu fom din ga hukumar.