Gobe za a fara gasar cin kofin kalubale na Nahiyoyi

Agobe Asabar 15 ga watan Yuni ake sa ran fara gasar cin kofin kalubale na Nahiyoyi (Confederation Cup)  a kasar Brazil.Gasar wacce Najeriya na daya daga cikin kasashe takwas da za su fafata saboda lashe kofin Afirka da ta yi a farkon shekarar nan, za ta fafata ne da manyan kasashe ne irin su Sifen […]

Gobe za a fara gasar cin kofin kalubale na Nahiyoyi
Gobe za a fara gasar cin kofin kalubale na Nahiyoyi

Agobe Asabar 15 ga watan Yuni ake sa ran fara gasar cin kofin kalubale na Nahiyoyi (Confederation Cup)  a kasar Brazil.
Gasar wacce Najeriya na daya daga cikin kasashe takwas da za su fafata saboda lashe kofin Afirka da ta yi a farkon shekarar nan, za ta fafata ne da manyan kasashe ne irin su Sifen da Uruguay da kuma Tahiti a rukuni na biyu watau rukunin “B”.
A rukunin farko watau rukunin A akwai kasashe irin su Brazil mai masaukin baki da Japan da Medico da kuma Italiya.
Za a kammala gasar ce a ranar 30 ga watan Yuni, 2013 idan Allah Ya kaimu.
Duk kasar da ta lashe kofin za ta samu kyautar  kimanin Naira miliyan 600.