Gobe za a fara gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na mata

A gobe Asabar, 6 ga watan nan da muke ciki ne za a fara gasar cin kwallon kafa na duniya na mata a Kanada. kungiyar kwallon kafa ta Najeriya da aka fi sani da Super Falcons za ta fafata ne a rukunin D da kasashen Amurka da Sweden da kuma Australiya.A ranar Litinin ne Najeriya […]

Gobe za a fara gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na mata
Gobe za a fara gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na mata

A gobe Asabar, 6 ga watan nan da muke ciki ne za a fara gasar cin kwallon kafa na duniya na mata a Kanada.

kungiyar kwallon kafa ta Najeriya da aka fi sani da Super Falcons za ta fafata ne a rukunin D da kasashen Amurka da Sweden da kuma Australiya.
A ranar Litinin ne Najeriya za ta kece raini da kasar Sweden a wasan farko. Wasan zai gudana ne da misalin karfe 9 na dare agogon Najeriya.
kasashe 24 ne za su fafata a gasar da suka hada da mai masaukin baki Kanada, sai China da Newzealand da kuma Holland da aka kasafta su a rukunin A. Rukunin B ya kunshi kasashen Norway da Thailand da Jamus da Kwaddebuwa. Rukunin C kuma ya kunshiKamaru da Ekwado da Japan da Suwizilan. Rukunin D ya kunshi Najeriya da Amurka da Sweden da kuma Australiya. Rukunin E kuma akwai Brazil da Koriya ta Kudu da Sifen da kuma Costa Rica yayin da rukunin F kuma ya kunshi kasashen Faransa da Ingila da Kolombiya da kuma Mezico. Kenan kasashe uku ne Najeriya da Kwaddebuwa da Kamaru ne suke wakiltar Afirka a gasar.
Gasar za ta gudana ne a tsakanin ranakun 6 ga watan nan da muke ciki zuwa 30 ga watan Yuni.
Sai dai a tarihin gasar babu wata kasa daga Nahiyar Afirka da ta taba lashe kofin. A yankin Afirka Najeriya ce sahun gaba wajen lashe kofin Afirka a bangaren mata. Muna fata za su yi abin kirki a wannan karo a Kanada.

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram