Gobe za a fara gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na ’yan kasa da shekara 20
A gobe Asabar 30 ga watan nan da muke ciki ne za a fara gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na ’yan kasa da shekara 20 (U-20) a kasar New Zealand. kasashe hudu ne daga Afirka suka samu halartar gasar da suka hada da Najeriya da Ghana da Mali da kuma Senegal. Sannan kasashe […]

A gobe Asabar 30 ga watan nan da muke ciki ne za a fara gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na ’yan kasa da shekara 20 (U-20) a kasar New Zealand.
kasashe hudu ne daga Afirka suka samu halartar gasar da suka hada da Najeriya da Ghana da Mali da kuma Senegal. Sannan kasashe 24 ne daga sassan duniya za su fafata a gasar don neman wanda zai lashe kofin.
A ranar Litinin mai zuwa ne Najeriya za ta fara wasanta na farko da Brazil a rukunin E. Za a gudanar da wasan ne da misalin karfe 1 na rana agogon Najeriya.
Sai dai a ranar Asabar, watau a ranar da za a fara gasar ce ake sa ran mai masaukin baki New Zeland za ta fara wasan farko da Ukraine da misalin karfe daya na rana sai kuma wasan Amurka da Myanmar da su ma za su yi da misalin karfe 1 na rana. Sai wasan karshe da za a yi a ranar a tsakanin Ghana da Austria da misalin karfe 7 na dare.
Manu Garba shi ne kocin Najeriya kuma ya gayyaci ’yan kwallo kimanin su 21 da suka hada da: Masu tsaron gida uku (Goal keepers) da suka hada da Dele Alampasu da Joshua Inaholo da kuma Olorunleke Ojo. Sai bangaren masu tsaron baya (defence) da suka hada da: Chidiebere Nwakali da Musa Muhammad da Mustapha Abdullahi da Prince Omego da Wifred Ndidi da kuma Zaharaddeen Bello. A ’yan wasan tsakiya (midfielders) kuwa akwai Akinjide Idowu da Bernard Bulbwa da Godwin Sabiour da Ifeanyi Ifeanyi da Ifeanyi Mathew da Kelechi Iheanacho da Kingsley Sokari da kuma Musa Yahaya. Sai bangaren ’yan wasan gaba (Forwards) akwai Chidera Ezeh da Daddy Moses Simon da Isaac Success da kuma Taiwo Awoniyi.
Idan ba a manta ba kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 17 ce a karkashin koci Manu Garba ta lashe gasar cin kofin duniya na ’yan kasa da shekara 17 da ya gudana a Hadaddaiyar Daular Larabawa a shekarar 2013. Don haka ’yan kwallon da kocin ya gayyato a wannan karon don su fafata a matakin ’yan kasa da shekara 20 (U-20) a gasar sun hada da Dele Alampasu da Zaharaddeen Bello da Musa Yahaya da Kelechi Iheanacho.
Masana harkar kwallo sun ce da alama Najeriya ta tabuka abin-a-zo-a-gani a gasar musamman ganin yadda kocin ya gayyato zaratan matasan ’yan kwallon da za su fitar da Najeriya kunya a idon duniya. Fatarmu dai ita ce Allah Ya ba Najeriya da Afirka sa’a a wannan gasa.