Gobe za a fara gasar cin kofin matasa na Afirka

A gobe Asabar ne idan Allah Ya kaimu za a fara gudanar da gasar cin kofin Afirka na matasa  (U-23 AFCON).Za a gudanar da gasar ce a kasar Senegal.  Kuma wannan gasa ce za ta zama wani mataki na hayewa gasar Olamfik da za a yi a shekara mai zuwa a Brazil.Kocin kungiyar kwallon kafa […]

Gobe za a fara gasar cin kofin matasa na Afirka
Gobe za a fara gasar cin kofin matasa na Afirka

A gobe Asabar ne idan Allah Ya kaimu za a fara gudanar da gasar cin kofin Afirka na matasa  (U-23 AFCON).
Za a gudanar da gasar ce a kasar Senegal.  Kuma wannan gasa ce za ta zama wani mataki na hayewa gasar Olamfik da za a yi a shekara mai zuwa a Brazil.
Kocin kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Samson Siasia tuni ya tantance ’yan kwallon da zai tafi da su gasar.  Daga cikin ’yan kwallon da ya gayyato, hudu daga ciki suna yin kwallo ne a kasashen ketare (Professionals) yayin da sauran kuma suke kwallo a gida a kulob daban-daban.
Haka kuma babu dan kwallon kulob din Eyimba na Aba ko daya daga cikin ’yan kwallon.  Kocin ya cire sunayen ’yan kwallon Enyimba biyu ne da ya gayyato tun da farko watau Kingsley Sokari da Etor Daniel bayan sun bar sansanin horar da su a kwanakin baya ba tare da izini ba inda suka koma kulob din Enyimba suka buga wasan karshe a gasar rukunin firimiya, inda Enyimba ta samu nasarar lashe kofin a karo na bakwai. Da suka nemi dawowa ne sai kocin ya ki amincewa da su.
Haka kuma bictor Osimhen yana daga cikin ’yan kwallon da kocin ya gayyato.
Najeriya dai za ta fara wasanta ne a jibi Lahadi da kasar Mali kafin ta yi wasa na biyu da Masar (Egypt) a ranar 2 ga watan gobe sannan ta yi wasa na uku da Aljeriya a ranar 5 ga watan gobe (Disamba).
kasashe uku da suka fi nuna kwazo a gasar ce za su haye gasar Olamfik da za a yi a Brazil a shekara mai zuwa.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa