Gobe za a fara gasar firimiya ta Ingila

A gobe Asabar ne ake sa ran za a fara gasar rukuni-rukuni na firimiya na Ingila da aka fi sani da (2015-2016 English Barclays Premier League).A bara, kulob din Chelsea ce ke rike da kambun yayin da Manchester City da Arsenal da kuma kulob din Manchester United ke biye da ita bi-da-bi.Masu sha’awar kallon kwallon […]

Gobe za a fara gasar firimiya ta Ingila
Gobe za a fara gasar firimiya ta Ingila

A gobe Asabar ne ake sa ran za a fara gasar rukuni-rukuni na firimiya na Ingila da aka fi sani da (2015-2016 English Barclays Premier League).
A bara, kulob din Chelsea ce ke rike da kambun yayin da Manchester City da Arsenal da kuma kulob din Manchester United ke biye da ita bi-da-bi.
Masu sha’awar kallon kwallon kafa a akwatunan talabijin musamman a Najeriya ne ake sa ran za su yi tururuwar zuwa gidajen kallon kwallo don ganin yadda wasannin za su kaya.
Haka kuma a yau da gobe ne ake sa ran fara gasar rukuni-rukuni a kasashen Jamus da Italiya da Faransa. Amma a Sifen sai nan da makwanni biyu masu zuwa.

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram

An tsinci gawar wata mata babu kai a Abuja