Gobe za a fara gasar Polo ta bana a Katsina

A kalla kungiyoyi (Teams) goma sha takwas ne da suka fito daga manyan kungiyoyin wasan Polo takwas za su fatata a gasar kwallon Polo na shekara ta 2015 da za a fara gobe a Katsina.  An saba gudanar da irin wannan gasa ce a duk shekara a Katsina kuma ita ce  mabudin wasan Polo a […]

Gobe za a fara gasar Polo ta bana a Katsina
Gobe za a fara gasar Polo ta bana a Katsina

A kalla kungiyoyi (Teams) goma sha takwas ne da suka fito daga manyan kungiyoyin wasan Polo takwas za su fatata a gasar kwallon Polo na shekara ta 2015 da za a fara gobe a Katsina.  An saba gudanar da irin wannan gasa ce a duk shekara a Katsina kuma ita ce  mabudin wasan Polo a duk inda ake gudanar da wasan a cikin Najeriya. Masu buga wasan da suka fito daga Kaduna da Zariya da Bauchi da Yola da Minna da Fatakwal tare da babban birnin tarayya Abuja sai mai masaukin baki Katsina.
Manyan kofuna 4 ne ake sanya wa a don fafatawa a kansu domin samun nasarar cinye su a gasar. Babban kofi dai shi ne kofin Najeriya sai kofin Janar Hassan Usman Nagogo. Sauran su ne kofin Comassie da na Talba. Har ila yau akwai kananan kofunan da ake buga wasa a kansu kamar kofin tunawa da Sarki Dikko wanda shi ya fara kawo wwasan Polo kasar nan. Sai kofin Sa Usman Nagogo wanda shi ne ya fi kowa samun darajar nan ta a tara (+) a lokacin zamaninsa. Akwai kofin Shugaban kasa da kofin Gwamna da kofin Maidabino da kuma kofin Lawal Kaita wanda masu koyon wannan wasa ke yin gasa akansa. kungiyoyi irinsu Kaduna Kakumi da Nadabo Fam daga Bauchi da Abuja Guard Bridget da Minna Bosso da Katsina Kangiwa da AFDIN da Mikmash da sauransu ne za su shiga cikin wannan gasa ta bana.
Shahararrun ‘yan wasan da za su hallara sun hada da Bello Buba da Ibrahim dangaye da Umar Kabir da Hamisu Buba da Aliyu Hassan Hadeja da Ibrahim Abba da Muhammadu Usman Sarki. Sauran sun hada da Balaho da Aliyu MTN da Ibrahim U. Sarki da Dikko Mangal da Aminu Mashasha da sauransu.
Shugaban kungiyar kwallon Polo wanda kuma shin e tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna Alhaji Lawal Kaita ya ja hankalin ‘yan wasan da su cigaba da zama masu ladabi da biyayya kamar yadda aka sansu da hakan. Har ila yau ya bukaci su kara hada kai ga junansu tare da bin dokoki da ka’idodin wasan kasancewar wasa ne mai wahala saboda amfani da dabba a wajen yin sa. Shugaban ya kuma yi kira ga jama’a da su zamo masu da’a da zaman lafiya kamar yadda aka san Jihar ta Katsina akan zaman lafiya.
Shi kuwa kyaftin kungiyar Malam Umar Kabir kira ya yi ga ‘yan wasan da su rika fitowa a kan lokaci a duk lokacin da aka tsaya. Malam Umar har ila yau ya kara tunatar da ‘yan wasan akan irin abubuwan da ake bukata daga wajensu,wato tsare dokokin wasan tare da bin umarni.
 Shi kuwa Manajan gasar Alhaji Abdu Usman Nagogo cewa ya yi tuni suka gama tsara yadda gasar za ta kasance a tsakanin masu son shiga gasar. Sun kuma tanadi duk wasu kayan da ake bukata don aiwatar da wannan wasa cikin nasara. Baya ga gyaran fili, akwai batun tsaro da kuma na kiwon lafiya da sauran makamantansu.
Kazalika kungiyar Polon ta Katsina ta amince da nadin tsohon Sufeto Janar na ‘Yan sanda Alhaji Ibrahim Comassie a matsayin Mataimakin shugaban kungiyar (bice President)
Ita dai wannan gasa za a fara yinta ne daga gobe Asabar 5 zuwa 12 ga watan nan a filin wasan Polo na Sa Usman Nagogo da ke kofar ‘Yandaka da ke birnin Katsina.