Gobe za a fara jigilar maniyyata aikin Hajjin bana
Jami’in gudanarwa na shiyyar Arewa maso Yamma na Hukumar Hajji ta kasa (NAHCON), Alhaji Umar Bala, ya ce a gobe Asabar ake sa ran fara jigilar maniyyata aikin Hajjin bana daga sassan kasar nan.Alhaji Umar Bala ya bayayna haka ne bayan kammala taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajjin na shiyyar, a Kano. Ya […]
LONDON, ENGLAND – FEBRUARY 18: The Sultan of Sokoto, Mohamed Sa’ad Abubakar waits to meet Prince Charles, the Prince of Wales at Clarence House on February 18, 2009 in London. The Sultan is the titular ruler of Sokoto in northern Nigeria. He is the leader of approximately 70 million Nigerian and West African Muslims and […]

Jami’in gudanarwa na shiyyar Arewa maso Yamma na Hukumar Hajji ta kasa (NAHCON), Alhaji Umar Bala, ya ce a gobe Asabar ake sa ran fara jigilar maniyyata aikin Hajjin bana daga sassan kasar nan.
Alhaji Umar Bala ya bayayna haka ne bayan kammala taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajjin na shiyyar, a Kano.
Ya ce shirye-shirye sun yi nisa, inda aka kammala yarjejeniya da dukkanin hukumomi sama da 20 da suke ba da gudummawa a yayin aikin Hajji, tare da kammala yarjejeniya da kamfanonin jiragen sama, masu jigilar maniyyata zuwa kasa Mai tsarki. Ya yi kira ga daukacin jami’ai na sauran hukumomi su bayar da hadin kai domin cimma nasarar aikin.
Ya ce kamfanin jiragen sama na Mad ne zai yi jigilar maniyyatan Jihar Jigawa, sannan na Kabo zai dauki maniyyatan Jihar Bauchi, a yayin da jiragen Kabo da Mad da kuma Meridian za su yi jigilar maniyyatan
Jihar Kano.
Jami’in ya kara da cewa; “Hukumarmu ta fito da sabon katin lafiya mai launin ruwan dorawa, wanda ake hada shi da fasfo na maniyyata, kuma bankunan da aka amince da su za su fara aikin samar da kudin guzuri ga maniyyata nan ba da jimawa ba.”
Ya ce hukumar na kokarin ganin cewa maniyyat ba su fuskanci matsalar jinkirin tashi da kuma dawowa daga kasa Mai tsarki ba. Ya ce duk kamfanin jigilar da ya karya ka’idar da aka yi da shi, zai fuskanci
hukunci.
A jawabin Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa, Alhaji Sani Hassan Muhammad ya ce hukumarsa ta yi nisa wajen shirin aikin Hajjin bana, musamman wajen kama hayar gidaje masu inganci a kasa Mai tsarki.