Gobe za a rufe gasar kokawa a Nijar
Gasar cin takobi na wasan kokowar gargajiya ta 2014 da aka fara a ranar Asabar din makon jiya a Diffa da ke Jamhuriyar Nijar a gobe Asabar ake sa ran za a rufeta kuma ga dukkan  alamu za ta bar baya da kura.  Wannan gasar cin takobi da ake gudanarwa a Nijar a duk shekara […]
Gasar cin takobi na wasan kokowar gargajiya ta 2014 da aka fara a ranar Asabar din makon jiya a Diffa da ke Jamhuriyar Nijar a gobe Asabar ake sa ran za a rufeta kuma ga dukkan  alamu za ta bar baya da kura.
  Wannan gasar cin takobi da ake gudanarwa a Nijar a duk shekara wadda kuma kan zagaya a tsakanin jihohin kasar wadda a halin yanzu ake yinta a garin Diffa ta zo da batun da ya ba mafi yawan jama’a mamaki.
  Tun farko an sa ran ‘yan wasa 128 ne za su halarci garin na Diffa don fafatawa amma sai aka samu adadin da ba su kai haka ba sanadiyar korar wasu fitattun ‘yan kokowar da masu shirya wasan suka yi da sunan cewa ba ‘yan asalin Nijar ba ne cikinsu kuwa har da Aliyu Sallau na Jihar Zinder wanda kuma shi ne ke rike da takobin a halin yanzu.
Jami’an da ke gudanar da wasan sun ce sun dauki matakin fitar da ‘yan wasan da ba ‘yan asalin kasar ba ne don yin gyara a gasar.