Gobe za a rufe Gasar Wasanni ta Afirka a Maroko

A gobe Asabar idan Allah Ya kai mu za a kammala Gasar Wasanni ta Afirka karo na 12 a kasar Maroko. An fara gasar ce a ranar 19 ga wannan wata inda ake sa ran za a kammala a gobe Asabar 31 ga Agusta. Gasar tana gudana ce a manyan biranen kasar biyu wato Rabat […]

Gobe za a rufe Gasar Wasanni ta Afirka a Maroko

A gobe Asabar idan Allah Ya kai mu za a kammala Gasar Wasanni ta Afirka karo na 12 a kasar Maroko.

An fara gasar ce a ranar 19 ga wannan wata inda ake sa ran za a kammala a gobe Asabar 31 ga Agusta.

Gasar tana gudana ce a manyan biranen kasar biyu wato Rabat da kuma a Kasablanka inda kasashe 54 na Afirka suke halarta. Kimanin ’yan wasa 7000 ne suka halarci gasar inda hakan ya sa gasar ta fi kowace gasa yawan ’yan wasa a tarihi.

Tawagar Najeriya ce ta biyu mai dauke da ’yan wasa da jami’ansu kimanin 427.

Sai dai ba kowane wasa ne Najeriya ta fafata a kai ba.  Wasu daga cikin wasannin da Najeriya ta fafata a cikinsu sun hada da  kwallon Tennis da guje-guje da tsalle-tsalle da kwallon kafa na maza da mata da kwallon kwando da jifar mashi da tsallen ketare shinge da daga karfe mai nauyi da sauransu.

Ana sa ran manyan baki irin su Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) Ahmad Ahmad da Shugaban Hadaddiyar Kungiyar Masu Wasanni a Afirka   (UCSA), Ahmed Naseer da kuma Ministan Wasanni na Masarautar Maroko,  Moulay Rachid da sauransu ne za su halarci bikin rufe gasar.

A watan Yulin bara ne Maroko ta samu damar daukar nauyin gasar bayan an kwace daga kasar  Ekuatorial Guinea.