Gobe za a yi bikin wankan Sarki Kano Muhammadu Sanusi II
A gobe Asabar ce za a yi bikin wankan nadin sarautar Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano na 14. A yayin bikin na gobe, wanda ake sa ran zai tara dinbim mutane da suka hada da sarakunan gargajiya, hamshakan ma’aikata daga sassa daban-daban na kasar nan da kuma sauran al’umma, zai kasance mai tarihi, […]
A gobe Asabar ce za a yi bikin wankan nadin sarautar Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano na 14.
A yayin bikin na gobe, wanda ake sa ran zai tara dinbim mutane da suka hada da sarakunan gargajiya, hamshakan ma’aikata daga sassa daban-daban na kasar nan da kuma sauran al’umma, zai kasance mai tarihi, musamman ganin yadda al’umma suka yi na’am da kasancewarsa wanda ya gaji Sarki Ado Bayero.
A bikin, Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ne zai mika masa sandar sarauta, wanda haka zai tabbatar da kasancewarsa cikakken sarkin Kano na 14 a mulkin Fulani.
Tun da farko dai, an ambata nada shi sarkin ne a ranar takwas ga Yunin bara, inda Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Injiniya Rabi’u Sulaiman Bichi ya bayar da sanarwar amincewa da zabensa, kwana biyu bayan rasuwar Alhaji Ado Bayero.
Kafin a kai ga haka, an yi ta yada jita-jita a kafofin zumunci na intanet cewar an nada Chiroman Kano, Alhaji Sunusi Lamido Ado Bayero, babban dan marigayi, abin da har sai da gwamnati ta fito ta karyata wannan labarin.
Sabon sarkin na Kano dai sanannen ma’aikacin banki ne wanda ya shahara har ya zamo Gwamnan Babban Bankin Najeriya.
Kafin zamowarsa sarkin Kano, ya shiga takun-saka da Gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan, a kan wasu kudaden da ya yi zargin cewa sun bace a ma’aikatar man fetur. Wannan takaddama ta sa gwamnati ta tube shi daga kan mukaminsa.
An haifi sabon sarki Muhammadu Sanuni II a Kano, a ranar 31 ga watan Yuli, 1961. Ya samu digirinsa na farko a fannin tsimi da tanadi da kuma fannin shari’ar Musulunci daga Jami’ar Amadu Bello da ke Zariya da kuma Jami’ar Khartoum da ke Sudan.
Bayan ya koyar da tsimi da tanadi tsawon shekaru biyu a Jami’ar Ahmadu Bello Zariyaa, sai ya soma aikin banki a shekarar 1985 tare da ICON Limited, daga bisani kuma yai aiki tare da bankin UBA da kuma First Bank.
Ya kai matsayin Babban-Darakta a bankin na First Bank, wanda shi ne banki mafi girma a Najeriya a watan Janairun shekarar 2009, daga bisani kuma aka nada shi Gwamnan Babban Bankin Najeriya na 10 a watan Yunin shekarar 2009.
Mahaifinsa Muhammadu Lamido Sanusi ya rike mukamin Babban-Sakatare a Ma’aikatar Harkokin kasashen Wajen Najeriya, bayan ya rike mukamin Jakadan Najeriyar a kasashen Canada da Belgium da China.
Shi ne kuma jikan Sarkin Kano na 11, Alhaji Muhammadu Sanusi, wanda shi ne ma dalilin da ya sanya yake amsa sunan Muhammadu Sanusi II.