Gobe za a yi karon-battar birnin Manchester

A gobe Asabar ce ake sa ran za a yi wasa mai zafi a tsakanin kulob din Manchester City da Manchester United a gasar Premier ta Ingila. Wasan zai gudana ne a filin wasa na City da aka fi sani da Etihad Stadium da misalin karfe 6:30 na yamma agogon Najeriya. Masana kwallo suna ganin […]

Gobe za a yi karon-battar birnin Manchester

Manchester City da Manchester Utd

A gobe Asabar ce ake sa ran za a yi wasa mai zafi a tsakanin kulob din Manchester City da Manchester United a gasar Premier ta Ingila.

Wasan zai gudana ne a filin wasa na City da aka fi sani da Etihad Stadium da misalin karfe 6:30 na yamma agogon Najeriya.

Masana kwallo suna ganin wasan zai yi zafi ganin kawo yanzu kulob din City wanda ya lashe gasar sau biyu a jere yana fuskantar kalubale kamar yadda kulob din Manchester United yake fuskantar kalubale.

Wannan shi ne wasa karo na 16 kuma saura wasa uku a kammala zagayen farko don haka duk kungiyar da ta yi sake aka doke ta to za a ba ta tazara.

Tuni manajojin kungiyoyin biyu wato Pep Guardiola na City da Solksjaer na United suka shirya tunkarar wannan wasa.