Gobe za a yi zaben cike gurbi a Katsina
A gobe Asabar ake sa ran za a fafata a zaben cike-gurbi na kujerar Majalisar Wakillai daga karamar Hukumar Katsina bayan rasuwar Sheikh Umar da ya lashe a zaben a watan Maris din bana a karkashin Jam’iyyar APC.Fitattun ’yan takarar da za su fafata a zaben na gobe akwai Sani Aliyu danlami wanda Jam’iyyar APC. […]
A gobe Asabar ake sa ran za a fafata a zaben cike-gurbi na kujerar Majalisar Wakillai daga karamar Hukumar Katsina bayan rasuwar Sheikh Umar da ya lashe a zaben a watan Maris din bana a karkashin Jam’iyyar APC.
Fitattun ’yan takarar da za su fafata a zaben na gobe akwai Sani Aliyu danlami wanda Jam’iyyar APC. dan takarar wanda matashi ne mai shekara 35 an haife shi a garin Katsina, yana da Diploma, kuma dan kasuwa ne, da ya fara harkokin siyasa tun a lokacin Jam’iyyar APP.
Alhaji Sani ya yi takarar mukamai da dama da suka hada da na kansila da dan majalisar jiha, kuma ya taba zama Sakataren Mulki na Jam’iyyar CPC a Jihar Katsina.
Sai Dokta Muntari Kabir Usman dan takarar Jam’iyyar PDP, mai kimanin shekara 43 kuma dan marigayi Sarkin Katsina Alhaji Kabir Usman Nagogo. Dokta Muntari ya yi aiki a banki da kamfanin jaridar Leadership kafin ya tafi kasar Malesiya don ci gaba da karatu da koyarwa. Dokta Muntari ya fara harkokin siyasa ne a lokacin marigayi Shugaban kasa Umaru ’Yar’aduwa. Bayan shafe shekara bakwai a kasar waje ne ya yanke shawarar dawowa gida don bayar da tasa gudunmuwar.