Gobe za a yi zaben dan Majalisar Jihar Kaduna na Mazabar Lere

A gobe Asabar ce Hukumar Zabe ta kasa (INEC) za ta gudanar da zaben cike gurbi na dan Majalisar Dokoki ta Jihar Kaduna a Mazabar Lere ta Yamma da ke karamar Hukumar Lere.Za a gudanar da zaben cike gurbin ne, bayan da kotu ta soke zaben dan majalisa mai wakiltar mazabar Alhaji Muhammad Kabir Doka […]

Gobe za a yi zaben dan Majalisar Jihar Kaduna na Mazabar Lere
Gobe za a yi zaben dan Majalisar Jihar Kaduna na Mazabar Lere

A gobe Asabar ce Hukumar Zabe ta kasa (INEC) za ta gudanar da zaben cike gurbi na dan Majalisar Dokoki ta Jihar Kaduna a Mazabar Lere ta Yamma da ke karamar Hukumar Lere.
Za a gudanar da zaben cike gurbin ne, bayan da kotu ta soke zaben dan majalisa mai wakiltar mazabar Alhaji Muhammad Kabir Doka na Jam’iyyar APC, sakamakon karar da Dokta Mato Dogara na Jam’iyyar PDP ya kotun.
Da yake jawabi a wajen wani taron da ya yi da jami’an tsaro da wakilan jam’iyyu da sarakunan yankin kan zabe da za a gudanar a ofishin Hukumar INEC a garin Saminaka, Babban Jami’in
Hukumar a karamar Hukumar Lere, Malam  Muhammad Jibrin Yalo ya ce ’yan takara hudu ne za su fafata a zaben cike gurbi na gobe.
Ya ce ’yan takarar su ne Bashir Gatari Idris na Jam’iyyar APC da Dokta Mato Dari Dogara na PDP da Mu’azu Ahmed na PDM da kuma Jamilu Yakubu Sulieman na ACPN.
Ya ce hukumar ta kammala duk shirye-shiryen don gudanar da zaben kuma ya yi kira ga jama’ar yankin su fito su kada kuri’arsu cikin kwanciyar hankali tare da ba da goyon baya da hadin kai ta hanyar bin ka’idojin da hukumar zaben ta gabatar domin a yi zaben lafiya.