Gobe za a yi zaben kananan hukumomin Kano
A gobe Asabar ne za a gudanar da zaben kananan hukumomin Jihar Kano kamar yadda Hukumar Zabe ta Jihar (KAINSEC) ta bayyana. Alhaji Isma’ila Idris Rimin Gado, Kwamishinan Wayar da kan Jama’a na Hukumar ya shaida wa manema labarai cewa tuni hukumar ta samar da duk kayayyakin aikin da ake bukata don gudanar da zaben. […]
A gobe Asabar ne za a gudanar da zaben kananan hukumomin Jihar Kano kamar yadda Hukumar Zabe ta Jihar (KAINSEC) ta bayyana. Alhaji Isma’ila Idris Rimin Gado, Kwamishinan Wayar da kan Jama’a na Hukumar ya shaida wa manema labarai cewa tuni hukumar ta samar da duk kayayyakin aikin da ake bukata don gudanar da zaben. “Mun tanadi dukkan kayayyakin da ake bukata a wajen zabe, kamar takardun zabe da tawada da akwatunan zabe inda za mu rarraba su ga mazabu 484 da ke kananan hukumomi 44 na jiha,” inji shi. Ya ce gidajen rediyo biyar na jihar Hukumar KAINSEC ta yarje su sanar da sakamakon zaben, wato Gidan Rediyon Jihar Kano da Freedom da Rahama da Wazobiya da Edpress. Aminiya ta gano jam’iyyu uku ne suka shiga zaben wato Jam’iyyar APC mai mulkin jihar da babbar jam’iyyar adawa ta PDP da kuma Labour Party. Jam’iyyun PRP da PDM da wasu sun yi karar hukumar a kotu saboda kin sanya su a cikin jam’iyyun da za su tsaya takara a zaben, lamarin da hukumar ta karyata. Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta yi barazanar harbe duk wanda aka kama ya saci akwatin zabe a zaben na gobe.