Godiya da yabo domin alherin Ubangiji

Da zuciya daya nake gode maKa, ya Ubangiji! Ina rera wakar yabonKa a gaban alloli. Na durkusa a gaban tsattsarkan Haikalinka ina yabon sunanKa. Saboda madawwamiyar kaunarKa da amincinKa, Saboda Ka nuna daukakarKa da umarninKa. Ka amsa mini sa’ar da na yi kira gare Ka, Da karfinKa Ka karfafa ni. Dukkan sarakunan duniyar nan za […]

Godiya da yabo domin alherin Ubangiji
Godiya da yabo domin alherin Ubangiji

Da zuciya daya nake gode maKa, ya Ubangiji! Ina rera wakar yabonKa a gaban alloli. Na durkusa a gaban tsattsarkan Haikalinka ina yabon sunanKa. Saboda madawwamiyar kaunarKa da amincinKa, Saboda Ka nuna daukakarKa da umarninKa. Ka amsa mini sa’ar da na yi kira gare Ka, Da karfinKa Ka karfafa ni. Dukkan sarakunan duniyar nan za su yabe Ka, ya Ubangiji! Gama sun riga sun ji alkawarinka. Za su rera waka a kan abin da Ubangiji ya yi, Za su rera waka kuma a kan daukakarSa mai girma. Koda yake Ubangiji Yana can Sama, Duk da haka Yana kulawa da masu kadaici. Masu girman kai kuwa ba za su iya boye kansu daga gare Shi ba. Ko lokacin da nake tsakiyar wahala, Za Ka kiyaye ni lafiya, Ka yi gaba da abokan gabana, wadanda suka fusata, Za ka kuwa cece ni da ikonKa. Za Ka aikata kowane abu da Ka alkawarta mini, Ya Ubangiji! Kaunarka madawwamiya ce har abada. Ka cikata aikin da Ka fara.

Yabo ya tabbata ga Ubangiji! Ku yabi Ubangiji daga sama, Ku da kuke zaune a tuddan sama. Ku yabe Shi dukkanku mala’ikunSa, Ku yabe Shi, ku dukkan rundunarsa na sama! Ku yabe Shi, ku rana da wata, Ku yabe Shi, ku taurari masu haskakawa! Ku yabe Shi, ku sammai mafiya tsayi duka! Ku yabe Shi, ku ruwayen da kuke bisa sararin sama! Bari su duka su yabi sunan Ubangiji! Ya umarta, sai suka kasance.Ta wurin umarninSa aka kafa su A wurarensu har abada, Ba su kuwa da ikon ki. Ku yabi Ubangiji daga duniya, Ku yabi Ubangiji, ku dodannin ruwa da dukkan zurfafan teku. Ku yabe Shi, ku walkiya da kankara da dusar kankara, da giza-gizai da karfafan iska wadanda suke biyayya da umarninsa! Ku yabe Shi, ku tuddai da duwatsu, Da itatuwa ’ya’ya da kurama. Ku yabe Shi dukkanku dabbobi, na gida da na daji, Masu rarrafe da tsuntsaye! Ku yabe Shi, ku sarakuna da dukkan kabilu, Ku yabe Shi, ku shugabanni da dukkan hukumomi. Ku yabe shi ku samari da ’yan mata! Ku yabe Shi, ku tsoffafi da yara! Bari dukkansu su yabi sunan Ubangiji, SunanSa ya fi dukkan sauran sunaye girma, DaukakarSa kuwa tana bisa duniya da samaniya! Ya sa al’ummarSa ta yi karfi, Domin dukan jama’arSa su yabe Shi jama’arSa Isra’ila, wadda Yake kauna kwarai! Yabo ya tabbata ga Ubangiji!

Zan yi shelar girmanka, ya Allahna, Sarkina! Zan yi maKa godiya har abadan abadin.Kowace rana zan yi maKa godiya, Zan yabe Ka har abada abadin. Ubangiji Mai girma ne, dole ne a fifita yabonSa, GirmanSa ya fi karfin ganewa. Za a yabi abin da Ka aikata daga tsara zuwa tsara, Za su yi shelar manya-manyan ayyukanKa. Mutane za su yi magana a kan darajarKa da daukakarKa, Ni kuwa zan yi ta tunani a kan ayyukanKa masu ban-mamaki. Mutane za su yi magana a kan manya-manyan ayyukanKa, Ni kuwa zan yi shelar girmanKa. Za su ba da labarin girmanKa duka, Su kuma rera waka a kan alherinKa. Ubangiji Mai kauna ne, Mai jinkai, Mai jinkirin fushi, Cike da madawwamiyar kauna. Shi mai alheri ne ga kowa, Yana juyayin dukkan abin da ya halitta. Ya Ubangiji! Talikanka duka za su yabe ka, Jama’arka kuma za su yi maka godiya! Za su yi maganar darajar mulkinKa, Su ba da labarin ikonKa, Domin haka dukkan mutane za su san manyan ayyukanKa, Da kuma darajar daukakar mulkinKa. MulkinKa, madawwamin mulki ne, Sarki ne kai har abada. Ubangiji Yakan taimaki dukkan wadanda suke shan wahala, Yakan ta da wadanda aka wulakanta. Dukkan masu rai suna sa zuciya gare shi, Yana ba su abinci a lokacin da suke bukata, Yana kuwa ba su isasshe, Yakan biya bukatarsu duka.Ubangiji Mai adalci ne a abin da Yake yi duka, Mai jinkai ne a ayyukansa duka.Yana kusa da dukkan wadanda suke kira gare Shi, Wadanda suke kiranSa da zuciya daya. Yakan biya bukatar dukkan wadanda suke tsoronSa, Yakan ji kukansu, Ya cece su. Yakan kiyaye dukkan wadanda suke kaunarSa, Amma zai hallaka mugaye duka. A kullum zan yabi Ubangiji, Bari talikai duka su yabi sunanSa Mai tsarki har abada!

Yabo ya tabbata ga Ubangiji! Ka yabi Ubangiji, ya raina! Zan yabe Shi muddin raina. Zan rera waka ga Allahna dukkan kwanakina. Kada ka dogara ga shugabanni, Ko kowane mutum da ba zai iya cetonka ba. Sa’ar da suka mutu sai su koma turbaya, A wannan rana dukkan shirye-shiryensu sun kare. Mai farin ciki ne mutumin da Allah na Yakubu ne Yake taimakonsa, Yana kuma dogara ga Ubangiji Allahnsa, Wanda Ya halicci sama da duniya da teku, Da dukan abin da yake cikinsu. Kullum Yakan cika alkawarinSa. A yanke shari’arSa takan ba wanda aka zalunta gaskiya. Yana ba da abinci ga mayunwata. Ubangiji Yakan kubutar da daurarru. Yakan ba makafi ganin gari. Yakan daukaka wadanda aka wulakanta. Yana kaunar jama’arSa, adalai. Yakan kiyaye baki wadanda suke zaune a kasar. Yakan taimaki gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu da marayu. Yakan lalatar da dabarun mugaye. Ubangiji Sarki ne har abada! Ya Sihiyona! Allahnki zai yi mulki har dukan zamuna! Yabo ya tabbata ga Ubangiji!

(Zabura 138, 145 &146)