Godiya ga Ubangiji saboda madauwamiyar kaunarSa

Godiya ta tabbata ga Ubangiji domin wannan zarafi da Ya ba mu a yau domin mu yi nazari a kan nuna maSa godiya. A mokon jiya mun ga dai hanyoyin da ya kamata mu nuna wa Ubangiji Allah godiya – a cikin kowace hali. A yau, za mu ga yadda marubucin Zabura ya bayyana mana […]

Godiya ga Ubangiji saboda madauwamiyar kaunarSa
Godiya ga Ubangiji saboda madauwamiyar kaunarSa

Godiya ta tabbata ga Ubangiji domin wannan zarafi da Ya ba mu a yau domin mu yi nazari a kan nuna maSa godiya.

A mokon jiya mun ga dai hanyoyin da ya kamata mu nuna wa Ubangiji Allah godiya – a cikin kowace hali. A yau, za mu ga yadda marubucin Zabura ya bayyana mana cewa dole ne mu gode wa Ubangiji domin girmanSa da madauwamiyar  kaunarSa.

Zabura 107,138

Ku gode wa Ubangiji, gama Shi nagari ne, Kaunarsa madauwamiya ce!

Ku zo mu yabi Ubangiji tare, Dukanku wadanda Ya fansa, Gama Ya kwato ku daga makiyanku. Ya komo da ku daga kasashen waje, Daga gabas da yamma, kudu da arewa.

Wadansu suka yi ta kai da kawowa a hamada inda ba hanya, Sun kasa samun hanyar da za ta kai su garin da za su zauna a ciki.

Suka yi ta fama da yunwa da kishirwa, Suka fid da zuciya ga komai.

Cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji, Ya kuwa cece su daga wahalarsu.

Ya fisshe su, Ya bi da su sosai, Zuwa birnin da za su zauna.

Dole ne su gode wa Ubangiji saboda madauwamiyar kaunarSa, Sabili da abubuwa masu ban-mamaki wadanda ya aikata dominsu!

Ya shayar da wadanda suke jin kishirwa, Ya kuma kosar da mayunwata da alheranSa.

Wadansu suna zaune cikin duhu da inuwar mutuwa, ’Yan sarka suna shan wahala da sarkoki,

Saboda sun tayar, sun ki bin umarnin Allah Madaukaki, Sun kuwa ki koyarwarSa.

Suka gaji tikis saboda tsananin aiki, Za su fadi kasa, ba mataimaki.

A cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji, Ya kuwa cece su daga wahalarsu.

Ya fisshe su daga cikin duhu da inuwar mutuwa, Ya tsintsinka sarkokinsu.

Dole su gode wa Ubangiji saboda madauwamiyar kaunarSa, Sabili da abubuwa masu ban-mamaki wadanda ya aikata dominsu.

Ya kakkarya kofofin da aka yi da tagulla. Ya kuma ragargaza kyamaren da aka yi da bakin karfe.

Wadansu suka yi ciwo sabili da zunubansu, Suna ta shan wahala saboda muguntarsu.

Ba su so su ga abinci, Sun kusa mutuwa.

A cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji, Ya kuwa cece su daga azabar da suke sha.

Da umarninSa Ya warkar da su, Ya cece su daga kabari.

Dole su gode wa Ubangiji saboda madauwamiyar kaunarSa, Sabili da abubuwa masu ban-mamaki wadanda Ya aikata dominsu.

Dole su gode maSa, su mika masa hadayu, Su rera wakokin murna, Su fadi dukan abin da Ya yi!

Wadansu suka yi tafiya a teku da jirage, Suna samun abin zaman garinsu daga tekuna.

Suka ga abin da Ubangiji Ya aikata, AyyukanSa masu ban-mamaki wadanda Ya yi a tekuna.

Ya ba da umarni, sai babbar iska ta tashi, Ta fara hurowa, ta sa rakuman ruwa su tashi.

Aka daga jiragen ruwa sama, Sa’an nan suka tsunduma cikin zurfafa. Da mutanen suka ga irin hadarin da suke ciki, Sai zuciyarsu ta karaya.

Suka yi ta tuntuɓe suna ta tangadi kamar bugaggu, Gwanintarsu duka ta zama ta banza.

Cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji, Ya kuwa cece su daga azabarsu.

Ya sa hadari ya yi tsit, Rakuman ruwa kuma suka yi shiru.

Suka yi murna saboda wurin ya yi shiru, Ya kuma kai su kwatar jiragen ruwa lafiya, Wurin da suke so.

Dole su gode wa Ubangiji saboda madauwamiyar kaunarSa, Sabili da abubuwa masu ban-mamaki wadanda Ya aikata dominsu.

Dole su yi shelar girmanSa cikin taron jama’a, Su kuma yabe shi a gaban majalisar dattawa.

Ubangiji Ya sa koguna suka kafe kakaf, Ya hana maɓuɓɓugai su gudana.

Ya mai da kasa mai dausayi ta zama mai gishiri, marar amfani, Saboda muguntar wadanda suke zaune a can.

Ya sāke hamada ta zama tafkunan ruwa, Ya kuma mai da busasshiyar kasa ta zama maɓuɓɓugai masu gudana.

Ya bar mayunwata su zauna a can, Suka kuwa gina birni don su zauna a ciki.

Suka shuka gonaki suka dasa kurangar inabi, Wadanda suka ba da amfani mai yawan gaske.

Ya sa wa jama’arsa albarka, Suka kuwa haifi ’ya’ya da yawa. Bai bar garkunan shanunsu su ragu ba.

Sa’ar da aka ci nasara a kan jama’ar Allah, Aka kaskantar da su ta wurin mugun zalunci, Da wahalar da aka yi musu.

Sai Allah Ya wulakanta wadanda suka zalunci jama’arsa. Ya sa su suka yi ta kai da kawowa A hamada inda ba hanya.

Ya tsamo masu bukata daga cikin bakin cikinsu, Ya sa iyalansu suka riɓanya kamar garkunan tumaki.

Da adalai suka ga wannan, sai suka yi murna, Mugaye kuwa aka rufe bakinsu.

Da ma a ce masu hikima za su yi tunani a kan wadannan abubuwa, Da ma kuma su yarda da madauwamiyar kaunar Ubangiji.

Da zuciya daya nake gode maka, ya Ubangiji, Ina rera wakar yabonKa a gaban alloli.

Na durkusa a gaban tsattsarkan Haikalinka ina yabon sunanKa. Sabili da madauwamiyar kaunarKa da amincinKa, Saboda Ka nuna daukakarKa da umarninKa.

Ka amsa mini sa’ar da na yi kira gare Ka, Da karfinKa Ka karfafa ni.

Dukan sarakunan duniyar nan za su yabe Ka, ya Ubangiji, Gama sun riga sun ji alkawuranKa.

Za su rera waka a kan abin da Ubangiji Ya yi, Za su rera waka kuma a kan daukakarSa mai girma.

Ko da yake Ubangiji Yana can sama, Duk da haka yana kulawa da masu kadaici. Masu girman kai kuwa ba za su iya ɓoye kansu daga gare Shi ba.

Ko lokacin da nake tsakiyar wahala, Za Ka kiyaye ni lafiya, Ka yi gaba da abokan gabana, wadanda suka husata, Za Ka kuwa cece ni da ikonKa.

 

Za ka aikata kowane abu da Ka alkawarta mini, Ya Ubangiji, kaunarKa madauwamiya ce har abada. Ka cikata aikin da Ka fara.

Godiya ta tabbata ga Ubangiji.