Gogoriyo tsakanin matan Gwamna Tambuwal: Kishi ko neman suna?
Matan Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal biyu, Hajiya Mariya da Hajiya Maryam Mairo sun tsunduma cikin ayyukkan taimakon al’ummar jihar, inda a kusan kullum sai an samu daya daga cikinsu ta fita wurin wani taro ko rabon wasu kaya ko ziyarar jaje ko gaisuwar mutuwa ko duba marasa lafiya ko matan gari su […]
Matan Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal biyu, Hajiya Mariya da Hajiya Maryam Mairo sun tsunduma cikin ayyukkan taimakon al’ummar jihar, inda a kusan kullum sai an samu daya daga cikinsu ta fita wurin wani taro ko rabon wasu kaya ko ziyarar jaje ko gaisuwar mutuwa ko duba marasa lafiya ko matan gari su ziyarce su a gidajensu.
Kara-kaina da fadi-tashin da suke yi ne ya karkato da hankalin mutanen jihar gare su tare da tambayar kishi ne suke yi wa junansu ko neman suna.
“Duk ayyukkan da suke yi ana kallon kishi ne ke haddasa hakan domin ba wani bayani da na samu cewa amaryar ta taba kai ziyarar ban girma ga uwargida, duk da cewa ta ziyarci dukan dangin mijinta da ke Tambuwal da Sakkwato, kuma matan ba su taba tafiya tare don gudanar da wani aiki ba, duk da cewa nau’in aikinsu daya ne taimakon mata da kananan yara, abokan huldarsu a rabe suke,” inji wani dan rajin kare hakkin dan Adam a Jihar Sakkwato da bai so ambaci sunansa ba.
Wata ’yar aikin sa-kai a jihar ta ce: “Lamarin matan gwamnanmu neman suna ne kawai, in ka dubi ba ya kafin Gwamna ya zama Gwamnan Jihar Sakkwato ban taba ganin fuskar uwargidansa a kowane taro ba na siyasa da bukukuwa. Amma abin mamaki mijinta na darewa kujerar mulki aka fara ganinta cikin jama’a ta je nan ta ba da wannan. In ka koma wurin amaryarsa kuma ita gwana ce a harkar cinikayya amma a Arewa kaf ba ka jin sunanta sai da ta shigo gidan mulki.”
Malam Mukhtar Usman kuwa cewa ya yi: “Lamarin nan sabo ne a Jihar Sakkwato, da aka dawo mulkin dimokradiyya a 1999, tsohon Gwamna Bafarawa yana da mata uku amma daya ce gwamnatinsa ta ayyana a matsayin Uwargidan Gwamna, wato Hajiya Jamila Bafarawa, ita kawai ke mu’amala da jami’an gwamnati da tafiya tarurrukan mata. Bayan kammala shekarunsa takwas, tsohon Gwamna Wamakko yana da mata biyu gwamnatinsa ta ki ayyana dayarsu a amatsayin Uwargidan Gwamna haka suka yi zamansu a gida, jami’an gwamnati suna al’amuransu tare da Kwamishinar Harkokin Mata Hajiya Kulu Abubakar ita ke tara taron mata a siyasa ko aiki, har suka gama wa’adinsu. Da gwamnatin Tambuwal ta zo sai muka rika ganin matansa biyu suna shige-da-fice a wuraren taimakon jama’a, a yanzu ma matan sun fi Gwamnan zama a jihar da yin aiki, wannan sabo ne a siyasar jihar kuma zai taimaki jihar matukar suna yi don taimakon jama’a ne.”
kungiyoyin mata da suka hada da Nationalist Mobement reshen Jihar Sakkwato a karkashin jagorancin Hajiya Hadiza Tsalha Sidi da Mataimakiyarta Hajiya Inno Attahiru da shugabannin mata na Kwanni Ward da na barikin ’yan sandan kwantar da tarzoma Gidan Igwai a karkashin jagorancin Maimuna Mobayil sun kai ziyara ga Hajiya Mariya Aminu Tambuwal don jinjina mata kan ayukkan taimaka wa mata da take yi a jihar, yayin da ta matan ’yan sandan ta mika korafe- korafenta tare da nanata goyon bayansu ga gwamnatin jihar. Hajiya Mariya Tambuwal ta yi murna da zuwan kungiyoyin ta kuma ta yi alkawarin yin aiki da su don ciyar da matan jihar gaba.
Sannan ta ce za a duba koke-koken matan ’yan sandan kwantar da tarzomar musamman wadda dakinta ke zubar da ruwa kuma ta bab su tabbacin gwamnatin shirye take ta tallafa wa mata don inganta jin dadin rayuwarsu.
Haka kuma Hajiya Mariya Aminu Tambuwal da tawagarta sun ziyarci Asibitin Kula da Masu Ciwon Gaude da kananan yara ta noma, inda ta ba da tabbacin za a rika kula da marasa lafiya da yi masu aiki kyauta. Ta ce gwamnatin jihar a shirye take ta kula da lafiyar masu karamin karfi. “Dalilin ziyartar asibitin shi ne domin in gana da kwararrun likitocin da aka turo jihar nan don su yi wa mutanen da ke cikin mawuyacin hali aiki da ba su magani,” inji ta.
Daraktan Asibitin Dokta Bello Ahmad ya gode wa matar Gwamnan kan ziyara da biyan kudin aiki ga majinyata, inda ya ce likitocin sun zo ne daga kasashen Holand da Jamus. Sai ya zagaya da tagawarta ciki har da Kwamishinar Mata Hajiya Kulu Abdullahi Sifawa da matar Sakataren Gwamnatin Jihar Hajiya Balkisu Bashir Garba da Shugabar Matan Jam’iyyar APC da matan kwamishinoni da manyan sakatarori zuwa dakunan marasa lafiya.
Ita kuwa Hajiya Maryam Mairo Aminu Tambuwal ta kai ziyarar jajantawa ne kan gobarar da ta shafi Kasuwar Sabon Garin Kano da ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar Gwamnan Jihar Kano ga Uwargidan Gwamnan Jihar Kano Hajiya Hafsat Umar Ganduje.
A Sakkwato kuma ta kai ziyara a gidan yarin jihar inda ta tallafa da kayan masarufi da katifu da filoli da madara da magani domin saukakawa ga wadanda ke tsare. Kuma ta biya wa wasu mutane kusan 40 da bashi ya sanya aka a tsare su.
Ta ce ta yi haka ne saboda Musulunci yana son aikata alheri kuma za ta ci gaba da taimaka wa matasa maza da mata don kawo wa jihar ci gaba. Da Aminiya ta tuntubi kakakin Gwamnan, Malam Imam Imam kan a gwamnatance wace ce Uwargidan Gwamna a cikin matan biyu, sai ya ce gwamnati ba ta ayyana kowace uwargida (First Lady) ba. “A sanina ban taba jin lokacin da gwamnati ta ayyana sunan wata daga cikinsu a matsayin First Lady ba, a lokacinmu gaskiya babu First Lady,” inji Imam Imam.