Gogoriyon Gogarma da wakilan rafkiya

Shughaban wakilan rafkiya a Majalisar Haurobiya, Malam Tumbin-wulli, ya figita wadanda suka rike mukamin gogarma a kasr nan, inda ya bukaci su gabatar masa da batu na ingarman karfe kan yadda suka yi da damin Hauro tiren taliiya da suka wafto daga hannun masu fashi da mukami ko da dabara.Rubdigau da Mai-Fari-da idanu a bakar […]

Gogoriyon Gogarma da wakilan rafkiya

 Turmin dakan hauroShughaban wakilan rafkiya a Majalisar Haurobiya, Malam Tumbin-wulli, ya figita wadanda suka rike mukamin gogarma a kasr nan, inda ya bukaci su gabatar masa da batu na ingarman karfe kan yadda suka yi da damin Hauro tiren taliiya da suka wafto daga hannun masu fashi da mukami ko da dabara.Rubdigau da Mai-Fari-da idanu a bakar kwalba da Loma-a-murde ke fuskantar barazanar tumbin-wulli, don ya jajirce kan lalle su zo su yi cikakken batu kan yadda suka sarayar da dimbin dukiyar da suka wafto daga hannun kusu da jaba da gafiya. Har yanzu ba su bayyana a farfajiyar majalisar wakilan rafkiya ba.
Idan masu koyon watsattsake da buda wagagen littattafai da ke wannan farfajiya ta Dodorido, ba su ari faden Malam Mantau ba, za su fasko cewa mun taba gabatar da darasi mai taken “Kusu ya sabi kayan kusu,” inda muka yi batu kan yadda masu handama da babakere ke yin watanda da cinikin ta’asar tasar matan barawo. Ga dukkan alamu dai majalisar wakilan rafkiya na kokarin sake kwata ta’asar tasar matar barawo, musammann ganin yadda aka baje kolin damin Hauron da suke wawushewa daga lalitar kasar Haurobiya, da sunan abin biyan bashi (Allah ba ni in biya ba shi). dimbin damin da wakilan rafkiya ke rafkewa a kowace shekara ya fi karfin dukiyar kananan kasashen Yammacin Ifrikiyya. Ko dai wadannan wakilan na laluben kari ne? dangane da amsar wannan tambaya, sai mu dan tsahirta sai Gogarma Loma-a-murde ya kamala gogoriyo da badakalar kwashi-kwaraf da ake tafkawa a cikin wannan majalisa, don ta haka ne za mu fasko jirginsu.
Idan ma Rubdigau da Ma-Farida-da-idanu a bakar kwalba da Loma-a-murde sun salwantar da dukiyar berayen da suka karbo, ai bai kamata wakilan rafkiya su tayar da kayar baya, tunda su ma ana jinka musu. Kuma idan aka ce za a yi tonon-silili, za karge da yanayin “Kura na kiran kare maye.” Ko kuwa wasan mage da kadangare ake son yi, wato, inda ta ce “kadangare zo mu je wasa,” ya ce “ba za ni ba shegiya mage da kunnuwa sai ka ce fanke.”
A batu na ingarman karfe, ya kamata a yi wata doka da za ta bai wa gogarma karfin ikon dawo wa al’umma dukiyarsu da manyan kwabo a kasar Haurobiya suka wawushe. Sai dai babban abin takaicin shi ne Gogarma Loma-a-murde ya zama muzurun Lami. Kuma idan ya yi wasa za a lamushe shi. Al’ummar kasa kuwa wajibi ne su baza na-zomo, su kura na-mujiya, don ganin an daina salwantar da dukiyarsu, ta yadda Gwamnatin Jatau- mai-sa-in-sa za ta daina neman karfin kasafin Hauro ta bhaure da su; Gwamnonin Haurobiya su daina wawushe dukiyar kananan hukumomi; Hukumar Jan-gali, ta daina wawushe kudin Hauirobiya da sunan haraji, amma babu wanda ya ga aikin sisi, duk da cewa muna da Masanin Sisi-da-sisi, wanda a halin yanzu shi ne Gwamnan Babban asusun Haurobiya; shi ma an kusa mayar da shi Gwamnan Asusun karfanfana.
Dabara dai ta rake ga mai shiga kwakware, a daina waskiya wajen ririta damin Hauron Haurobiyawa. Kura ta daina kiran kare maye. Gogarma a je a ci gaba da gogoriyon artabun mage da bera.

Sakonnin makaranta:

Mu rubbanya ayyuka a wat amai alfarma

Assalamu Alaikum
Dukkan Godiya da jinjina sun tabbata ga Mai Duka, wanda ya yi sama da kasa ba tare da taimakon kowa ba, haka nan ya yi sama ba tare da dirkokin da suke rike da ita ba. AmincinSa ya kara tabbata ga Cikamakin Annabawa wanda ya zo mana da shiriya da hanyoyin karatu da ilimi.
Bayan gaisuwa irin ta masu bautar Fiyayyen Sarki daya tilo. Ina isar da babbar gaisuwata ga uban wannan makaranta Shaikh Malam Farfesa Dodo Uban Masu Karatu, da fatan an shiga ibadar azumi cikin nasara, haka ma ga daukacin daliban wannan makaranta mai albarka da tarin alkhairi na kasa dama na duniya baki daya.
‘Yan uwa na dalibai ina tunatarwar damu, da mu rika amfani da basirar da Allah ya horewa Uban Masu Karatu Farfesa Dodo, kamar yadda na tuna wata haduwa da muka yi da shi ya yi mana nasiha da mu riki wannan makaranta a matsayin wani waje da zai zama hanyar alkhairi gare mu da ‘yan uwanmu ta hanyar kyautata musu da taimaka musu yayin da bukatar hakan ta taso.
Wannan tasa na ke kira a garemu da kar watan azumi ya wuce ba mu ribanya ayyukanmu na lada ba, kar mu rena kyautar da za mu bawa dan uwanmu ko ‘yar uwarmu ko makwabcinmu ko abokinmu, duk kankartarta ko da tsagin dabino ne ka bayar domin ya zama ka karawa ladanka nauyi.
Kar na tsawaitaba da bayani na san tuni an je gano, ina yekuwa ga daliban Tumbin Giwa da mu kara jajircewa wajen gudanar da tafiyar makaranta.
 Na gode,
Umar Muhammad Abdullahi (Abban Haidar)
Shugaban daliban Jihar Tumbin Giwa, Na Riko.
08067676454, 08099767645.

Tsokaci kan batun direbobin alli a Jihar Bawan-cici

Assalamu Alaikum. Bayan gaisuwa irinta masu bautar Allah tare da fatan dukkan yan watsattsake da koyon bude wagagen littattafai suna nan lafiya. A gaskiya abun da ke wakana a kasar mu ta Haurobiyawa se a hankali, duk bangarori na rayuwa ba sauki, ga uwa-uba abin da mulaka’u suke yi daga tarayya zuwa jiha zuwa kananan hukumomi. Tabbas gyara daga  manya yake zuwa to amma manyan fa daga cikin mu za su fito. Yan uwa MU JI TSORON MAI-DUKA. ADAMU HASSAN. ME RIkON dALIBAI NA JIHAR BAWAN-CICIN MALLAM YA ISA YAYI GUDA. Muna godiya ga mallam game da rubutun makon da ya arce. Allah ya sa shugabannin mu su gane gaskiya.

Ta’aziyya ga Kamfanin buga amintattun jaridun Haurobiya

daya daga cikin dalibai ma’abota Sha’awar nutsewa tsundum cikin makarantar Malam-bude-mana-littafi yayi nazarin a karkashin Sharhinka Na ta’aziyya ga Editan Media Trust Malam Sulaiman Muh’d hakika mun yi rashi kuma muna fatan za mu koyar kamar yadda muka koya Allah Yasa za ku sakani cikin rukunin ma’abota ra’ayin budewa da nazarin wagagen litattafai. Sai na jiku. Na gode