Gogoriyon Gogarma ta kwaranye

Kowane Gagarma  a kasar Haurobiya  ya sha gwagwarmaya da arangama da masu fashi da mukami ko da dubara, tun daga zamanin mulkin Baba-ojo, mao gonakin Ottawa zuwa kan Gudun-loko, wanda ya kare jan-zarensa da Loma-a-murde.Ga shi nan tun da Loma-a-murde ya yunkura ya cafko uwargidan Saurayin-kirinki, har Mjalisar Tsofaffin Haurobiya ta kulla masa bita-da-kulli. Akwai […]

Gogoriyon Gogarma ta kwaranye
Gogoriyon Gogarma ta kwaranye

Kowane Gagarma  a kasar Haurobiya  ya sha gwagwarmaya da arangama da masu fashi da mukami ko da dubara, tun daga zamanin mulkin Baba-ojo, mao gonakin Ottawa zuwa kan Gudun-loko, wanda ya kare jan-zarensa da Loma-a-murde.
Ga shi nan tun da Loma-a-murde ya yunkura ya cafko uwargidan Saurayin-kirinki, har Mjalisar Tsofaffin Haurobiya ta kulla masa bita-da-kulli. Akwai yiwuwar Saurayin-kirinki ya bar karagar jagorancin majalisa tare da Loma-a-murde, musamman jin cewa ana zarginsa da hannun a kirkiro da jabun kundin dokokin majalisa, wanda aka samu a hannun Akuyar-maman-Daudu. Kodayake Dano Mai-alaye na kokarin kariya. Al’amarin dai kamar da wuya, wai ‘mace mai dingis-dingis da auren nesa.’
Dogarin Wakilan Rafkiya ka tsaya tsayin daka, karka kwakwayi tsofaffi. Ka bi Baban masu Buyrin-huriyya, don ceto kasar nan daga Samarin kusu da’yan matan jaba da gafiya.
A zamanin Baba-ojo, Gogarma Rubdigau ya yi arangama da jiga-jigan gwamnati amma wata sa’a jam’iyya mai dan boto da sanda jirge ta rika shinge samarin  kusu da ’yan mtan jaba da gafiya, don kada a garkame su. Wasansu kuwa a kan kange su ne daga hujuncion hukuma, saboda son ran miyagu a cikin al’umma.
Irin wannnan ta’ada ta tsunka tarkon smarin kusu da ’yan matan jabba da gafiya, ta sanya Gogarmiya Mai Fari da na-mujiya a cikin bkar kwalba ta bukaci a rika duba masu tabin kwanya a jerin jiga-jigan Gwamnatin Haurobiya, musamman ganin yadda suke jidar Hauro su haure da dami, tamkar masu yankar ciyawa da lauje.
Wani lamari mai faranta zuciya, shi ne, Gogoriyon Gogarma ya kwaranye, musamman a kwanaki sili da zagaye-zagaye na Gwamnatin Baban masu Burin-huriyya. Don haka idan aka bukaci in bijiro da nasarorin da Gwamnatin Jam’iyya mai magnain zogi da radadin ciwon kurungu, sai in ce an cafke dimbin wadanda suka kwashi gararuma, wasu kuwa sun firgita sun dawo da su.
Hakika mun gani a shafukan jaridu da makalu da mujallu, kai har ma da shafukan fuskantar Bokoko da Tuwon-titi, inda ka baje labarin wasu tsofaffin baraden Haurobiya mutum sili da kofar hanci da suka daura aniyar dawo da damin Hauro tiren-taliya da wuka wawushe a wajen sayen makaman tunkarar masu Haramta Bobo da kwambon bokoko.
Hasalima an yi hsashen cewa Mace-da-zane tsoron tuhuma ne ya haifar mata da laulayi har ta bararraje a karagar bokan-Turai da ake shimfidar da majiyata.
A matsayina na Direban Alli a farfajiyar Dodorido, na fasko cewa, Asararren Dokin-bobo ko Asarar-dankwabo da Tumfafin-falo sun tafka asara, inda aka kassara kwantiraginsu na kankane bututun man tunkuza.
Ga Samun-bom-da-sauki an gurfanar da shi a gaban kuliya kan mallakar kayan artabu ba bisa ka’ida ba. Ni dai ina kyautata hasashen cewa, wannan tsaohon mai bai wa Shugaban Jona-tantin-mulki shawara kan harkokin kariya ga kasa, ya tafka ta’asda a kwanon tasa. Uwa-uba kwananan nanj aka fasko jirgin Anyi-mimi, wand a halin yanzu muna iya kiransa Anya yimi Hauro. Domin wannan tsohon saka-kataren Gwamnatin Tarairayar Haurobiya ya haure da dami a wajen ginbin birnin karni, al’amarin da ya karke a zaman Birnin kari.
Haurobiya sun fasko jirgin masu wawushe damin Hauro daga lalitar kasar nan, don hana a gina farfajiyar Bokan-Turai da wurin koyon watsaytsake da buda wagagen littattafai. Ko ban kara wani abu ba, kowa ya gano cewa gogoriyon gogarma ya kwaranye, inda zai gudanar da aikinsa cikin sauki.
Batu na-dokin karfe shi ne a cikin kwanaki sili da zagaye-zagaye, Baban masu Burin-huriyya ya nuna wa Haurobiyawa cewa, ko babu Gogarma zai iya kwato damin Hauron da miyagun Haurobiyawa suka arce da shi. Kai hasali ma ba zai bari a yi gafiya ki sira da na bakinki ba. Akwai yiwuwar nan gaba kadan a tursasa kura ta mayar da abin da ta dundume kururunta.n Don haka giwa da zaki da suarn manyan dawa sai a yi hattara. Idan Gwamnatin Jam’iyyar maganin zogi da radadin kurungu za ta  iya hukunta manya da kananan kwari, to sai mu hakakke kan lallai Haurobiya ta hau turbar gyaruwa, sabanin yadda aka yi mana ’yan gyare-gyare irin n gyare da kurege. Shi ken an gogorriyon gogarma ya kwaranye!