Goje zai bayyana aniyarsa ta neman shugabancin majalisar dattawa

Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa, Sanata Muhammad Danjuma Goje, zai bayyana aniyarsa ta neman takarar kujerar shugaban Majalisar dattawa, bayan an amince da kudurin dokar kasafin kudi na shekarar 2019, wani daga cikin jigo a zauren majalisar dattawan Najeriyar ne ya shaidawa manema labarai hakan a yau. Sanatan, wanda ya bukaci a sakaya […]

Goje zai bayyana aniyarsa ta neman shugabancin majalisar dattawa

Sanata Muhammad Danjuma Goje

Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa, Sanata Muhammad Danjuma Goje, zai bayyana aniyarsa ta neman takarar kujerar shugaban Majalisar dattawa, bayan an amince da kudurin dokar kasafin kudi na shekarar 2019, wani daga cikin jigo a zauren majalisar dattawan Najeriyar ne ya shaidawa manema labarai hakan a yau.

Sanatan, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce Gojen, ya yi jinkiri akan bayyana aniyarsa na neman kujerar shugabancin majalisar dattawan, sakamakon yadda ya himmatu wajen ganin an amince da ayar dokar kasafin kudi na bana, wanda kwamitinsa ya ke aiki a kai.

Tunda farko dai Sanata Ahmed Lawan, dan jam’iyar APC daga jihar Yobe da kuma Sanata Ali Ndume, shi ma dan jam’iyar APC daga jihar Borno, sun riga sun ayyana manufarsu ta neman takarar kujerar shugaban majalisar dattawan.