Golden Eaglets za ta hadu da Brazil a wasan sada zumunta

kungiyar kwallon kafa ta U-17 da aka fi sani da Golden Eaglets za ta hadu da Brazil a wasan sada zumuntar da kasar Koriya ta shirya mai taken Suwon International Tournament. Gasar za ta gudana ne a tsakanin kasashe hudu kuma a cikin kwanaki hudu watau daga ranar 10 zuwa 14 ga watan nan da […]

Golden Eaglets za ta hadu da Brazil a wasan sada zumunta
Golden Eaglets za ta hadu da Brazil a wasan sada zumunta

kungiyar kwallon kafa ta U-17 da aka fi sani da Golden Eaglets za ta hadu da Brazil a wasan sada zumuntar da kasar Koriya ta shirya mai taken Suwon International Tournament. Gasar za ta gudana ne a tsakanin kasashe hudu kuma a cikin kwanaki hudu watau daga ranar 10 zuwa 14 ga watan nan da muke ciki.

kasashe hudu ne za su fafata a tsakaninsu da suka hada da mai masaukin baki Koriya da Brazil da Amurka da kuma Najeriya.
Za a yi wasan Brazil da Najeriya ne a ranar 10 ga watan nan da misalin karfe 10 na safe agogon Najeriya wanda ya yi daidai da karfe 6 na yamma agogon Koriya. Amma kafin wasan sai kasashen Koriya da Amurka sun barje gumi a wasan farko da misalin karfe bakwai na safe agogon Najeriya. Najeriya za ta hadu da Koriya ne a wasa na biyu yayin da Amurka kuma za ta kece raini da Brazil. Sannan Njaeriya za ta kece raini da Amurka ne a wasa na uku kafin Koriya ta hadu da Brazil a wasa na uku daga nan za a tantance kasar da ta samu nasara.
Wannan shi ne karo na biyu da Najeriya take halartar gasar. A shekarar 2007 Najeriya ta halarci gasar da aka yi a Koriya daga bisani ta lashe kofin duniya na ’yan kasa da shekara 17 da ya gudana a Koriya.

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram